BOKO HARAM: Rayukan mutum 10 aka rasa, 60 su ka ji rauni a harin Maiduguri

0

Akalla mutum 10 ne su ka rayukan su a wani harin bam da Boko Haram su ka kai mazabar Gwange, unguwar da ke bakin garin Maiduguri a ranar Talata.

Gwamna Babagana Zulum ya tabbatar da afkuwar mummunan harin.

Tara daga cikin mutum 10 da su ka rasa rayukan su din kananan yara ne da ke wasa a wani filin kwallo.

Sun mutu ne sanadiyyar bam din da ya tashi da su. Kuma akalla wadanda su ka ji raunuka sun kai mutum 60.

A wani sako da sojoji su ka aika ta ‘tes’, sun bayyana cewa sun fatattaki Boko Haram da su ka kai harin.

Sannan kuma sojin sun musanta mutuwar mutum biyar.

Rahoton PREMIUM TIMES na farko ya nuna cewa Boko Haram sun jefa bam a wani rukunin cinkoson jama’a a wata unguwa a Maiduguri, babban birnin Jihar Barno.

Gwamna Zulum ya ziyarci wasu asibitin da ake jiyyar wadanda su ka samu raunuka a harin bam din.

Jami’ai sun shaida wa Gwamna cewam mutum biyar ne su ka mutu, kuma wasu 60 su ka ji ciwo a harin bam din da aka harba da roket.

Mutum tara aga cikin 10 din da su ka rasa rayukan su duk kananan yara ne da a lokacin da aka harba masu roket din su na cikin wasan kwallo, a wani fillin kwallon unguwar Gwange.

Zulum ya yi bakin ciki da kuma ta’aziyya da alhinin wadanda su ka rasu. Sannan kuma ya jajanta wa wadanada su ka ji raunuka.

A lokacin da ya ke zagayen asibitocin da aka kwantar da wadanda aka ji wa ciwo, Zulum ya ce gwamnati za ta ba su kyakkyawar kulawa.

Kakakin Yada Labaran Zaratan Bakin Daga, wato ‘Theater Commanders’, Ado Isa, bai amsa kiran da wakilin PREMIUM TIMES ya yi mas aba, ballantana a ji ta bakin sa.

Share.

game da Author