Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 869 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba. Sannan kuma mutum 8 suka rasu a dalilin Korona a wannan rana.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa jihar Lagas ta samu karin mutum -229, Rivers-79, Taraba-73, Oyo-66, Ogun-60, FCT-58, Filato-56, Kwara-38, Ondo-38, Osun-24, Kano-22, Nasarawa-21, Abia-19, Edo-19, Akwa Ibom-19, Cross River-10, Delta-9, Benue-8, Ekiti-6, Borno-6, Katsina-4, Bauchi-3, Bayelsa-1 da Zamfara-1
Yanzu mutum 149,369 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 125,722 sun warke, 1,787 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 21,860 ke dauke da cutar a Najeriya.
Ranar Talata, mutum 1,368 suka kamu a Najeriya, jihohin Anambra, Oyo, Benue, Rivers da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –53,725, FCT–18,799, Filato –8,793, Kaduna–8,158, Oyo–6,564, Rivers–6,177, Edo–4,362, Ogun–3,865, Kano–3,558, Delta–2,498, Ondo–2,862, Katsina–2,021, Enugu–1,954, Kwara–2,713, Gombe–1,951, Nasarawa–2,144, Ebonyi–1,754, Osun–2,241, Abia–1,374, Bauchi–1,210, Borno-1,208, Imo–1,358, Sokoto – 767, Benue-1,170, Akwa Ibom–1,313, Bayelsa 723, Niger–895, Adamawa–725, Anambra–1,615, Ekiti–708, Jigawa 492, Taraba 657, Kebbi 306, Yobe-260, Cross River–252, Zamfara 219, Kogi–5.
Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko NPHCDA Faisal Shu’aib ya bayyana cewa za a yi wa mutum miliyan 109 allurar rigakafin cutar korona daga nan zuwa shekaru biyu masu zuwa.
Ya ce gwamnati na sa ran karban kwalaben maganin rigakafin miliyan 57 daga AVATT da COVAX da kuma wasu miliyan 1.5 da 100,000 wanda kamfanin MTN da kasar India suka baiwa Najeriya gudunmawa wanda za a yi amfani da su wajen yi wa wadanda suka dara shekaru 18 allurar rigakafin a kasar nan.
“Mata masu ciki, ma’aikatan kiwon lafiya, jami’an tsaro, tsofaffi da marasa lafiya ne za a yi wa rigakafin cutar da farko