KAKUDUBAR HUKUMAR NDDC: Minista Akpabio ya musanta zargin ya toshe bakin Minista Malami da Dala Milyan 5

0

Ministan Harkokin Bunkasa Yankin Neja Delta, Godswin Akpabio, ya musanta zargin cewa ya toshe bakin Ministan Shari’a Abubakar Malami da dala milyan biyar, domin a daga masa kafa a nada wanda ya ke so a nada shugabancin Hukumar Bunkasa Neja Delta (NDDC).

Ma’aikatar da Akpabio ke rike ce dai mai kula da ayyukan hukumar ta NDDC.

Idan ba a manta ba, an nada Effiong Akwa, wanda jiha daya ya fito da Akpabio, a matsayin Kantoman Rikon NDDC, bayan da Daraktan Kudi na hukumar da ke riko ya mutu sanadiyyar cutar korona a 2019.

Kabilar Ijaw sun rika yin zanga-zanga, bayan cire dukkan shugabannin hukumar da Shugaba Buhari ya yi, aka bar Akwa shi kadai, Sannan aka nada shi Kantoman Riko.

Da yawa daga cikin tsoffin shugabannin NDDC sun yi amanna cewa Akpabio ne ya haddasa korar shugabannin domin a nada Akwa wanda zai rika juyawa kamar waina, kuma su rika shiga daki su na kulla duk abin da su ka ga damar yi da kudin hukumar su biyu.

Su na ganin bai dace a nada Akwa ba, domin jiha daya ya fito da Akpabio, Minista na Ma’aikatar baki daya.

Ban Toshe Bakin Malami Da Kudi Ba -Akpabio

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Akpabio, mai suna Anietie Ekong ya fitar, ya ce karya ake yi Akpabio bai bada dala milyan biyar ga Minisan Shari’a Malami ba.

Sannan kuma ya yi barazanar zuwa yam aka duk wanda ya buga labarin a kotu.

Ya ce wadanda ba su gamsu da sakamakon bincike ba ne ke yada wannan sharrin a kan sa.

Minista Akpabio Ne Ya Fara Kafa Garken Masu Satar Kudin NDDC –Joy Nunieh

Cikin watan Yuli 2020 Tsohuwar Shugabar Riko ta Hukumar Raya Jihohin Neja Delta (NNDC), Joy Nunieh, ta yi ikirarin cewa Minista Akpabio ne ya fara kafa garken masu satar kudin NDDC.

Tsohuwar Shugabar Riko ta Hukumar Raya Jihohin Neja Delta (NDDC), Joy Nunieh, ta zargi Ministan Ma’aikatar Kula da Neja-Delta, Godswill Akpabio da harkallar satar makudan kudade.

Nunieh ta ce a cikin ‘yan watannin da ta yi ta na rikon-kwaryar hukumar, Minista Akpabio a matsayin sa na Ministan Neja-Delta, ya yi ta kokarin tirsasa ta yin rantsuwa a asirce cewa ba za ta fallasa duk wata cuwa-cuwa, harkalla, wuru-wuru, kamaya-maya, lodi da jidar kudaden da aka yi ko za a yi ba.

“Misali, akwai lokacin da ya ce min na shirya takardar bayar da kwangilar bogi ta raba kayan agaji ga al’ummar Neja-Delta da albaliyar ruwa ya yi wa barna.” Inji Nunieh.

Ma’aikatar Neja-Delta da Akpabio ke shugabanci dai ita ce ke kula da ayyukan Hukumar NDDC.

Tsohuwar shugabar ta NDDC, ta shaida wa manema labarai bayan ta fito daga bayyanar da ta yi a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Binciken NDDC cewa, da ta kuskura ta bi son ran Minista Akpabio ta yi duk abin da ya ke so ta rika yi, to da yanzu ta na can daure a kurkuku.

Ta ce Akpabio ya yi duk wani kokari domin ya tirsasa ta yin rantsuwar ba za ta tona masa asiri ba, amma ta ki.

Tuni wannan bidiyo da Gidan Talbijin na Channels ya nuna, ana ta watsa shi a soshiyal midiya.

Ta ce sau uku Akpabio ya na tirsasa ta domin ta yi rantsuwar ba za ta tona masa asiri ba.

Ta kara da cewa da ta ki yin rantsuwar-,kaffarar,-Akpabio, sai aka rangada fadar shugaban kasa aka gurfana a gaban Sarki Abba, Hadimin Shugaban Kasa a Harkokin Cikin Gida.” Shi ne ya sasanta mu.

Nunieh ta ce tsoro ta ji za ta iya zaman kurkukun shekara biyar cur idan Akpabio ya gina mata rijiya ta rufta.

Ta ce za a iya kama ta a karkashin Dokar Ka’idojin Bayar Da Kwangiloli. Alhali ba ta iya kare kan ta, shi kuma Akpabio ya tsallake rijiya abin sa.

“To sai bayan da na ki amincewa na yi wa Akpabio rantsuwar-kaffara ce sannan ya fara kulla tuggun ganin an cire ni daga kan mukamin.

“Ya ce sai ya cire ni. Daga nan kuma ya fara watsa farfagandar bata min suna da zubar min da kima.” Inji ta.

Kokarin da Premium Times ta yi domin jin ta bakin Kakakin Akpabio, Anietie Ekoong ya ci tura, domin har yau ba a maido amsar tes din da aka tura masa ba.

Takun-saka Tsakanin Akpabio Da Nunieh:

Nunieh ta zama Shugabar Rikon NDDC bayan an cire Akwagaga Enyia cikin Octoba 2019.

Sai dai kuma ita ma din an cire ta watanni hudu bayan nada ta, bayan rika samun bayanan salwantar makudan kudade.

Daga nan ne kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Kemebradikumo Pondei, a madadin ta.

Pondei ne a waccan Alhamis da ta gabata, ya shaida wa Kwamitin Bincike a Majalisar Dattawa cewa, sun kassafa naira bilyan 1.5 a tsakanin su, a matsayin tallafa wa kan su da agajin zaman gida lokacin Coronavirus.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Minista Akpabio ya kitsa algungumancin cire Nunieh daga shugabancin NDDC, aka nada Kemebradikumo.

Mutanen da ke da masaniyar takun-saka tsakanin Akpabio da Nuneih, sun ce mutanen biyu ba su jituwa a tsakanin su.

Yayin da ake tattaunawa da ita, ta ce Akpabio bai taba sa wa takardun ta hannu ba. Sai dai kawai ya hada baki da wasu ‘yan barandan sa su rika shirga karkallar fitar da makudan kudade.

“Ina sane na ki bin sa zuwa Taron Majalisar Zartaswa, domin na rigaya na san irin mummunar gidogar harkallar da ya shirya wa Shugaban Kasa. Na san Dokar Kwangila za ta iya kama ni da laifi, har a daure ni shekaru biyar.”

Nunieh ta ci gaba da bayyana dalla-dallar kwangilolin gidoga da Akoabio ya rika shiryawa. Kuma ta ce duk wasu kudade da za a fitar, sai da sanin sa.

Share.

game da Author