Uwargidan gwamnan jihar Legas Ibijoke Sanwo-Olu ta kadamar da sabbin motoci guda uku na tafi da gidanka domin yi wa mutane gwajin cutar tarin fuka a ko-ina suka a fadin jihar.
Ibijoke ta bayyana cewa motocin za su rika yawo jihar suna yi wa mutane gwajin cutar nan take da kuma basu magani kyauta.
Bayan haka Ibijoke ta ce gwamnatin jihar ta zuba na’urorin gwajin cutar a wasu zababbun asibitoci 18 dake jihar domin su rika yi wa mutane gwajin cutar da basu magani kyauta.
“Ina kira ga mutane da su yi amfani da wannan dama su yi gwajin cutar domin kyata ne kuma maganin ma kyauta za a ba ka.
Bincike ya nuna cewa a shekarar 2019 akwai mutum 38,277 dake fama da cutar ba tare da sanin gwamnati ba a jihar.
Sannan duk shekara cutar na kashe 245,000 kuma wasu 590,000 na kamuwa da cutar a Najeriya.
A watan Nuwambar PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarain tallafin da asusun bada tallafi na duniya wato Global fund, ya baiwa Najeriya zunzurutun kudi har dala miliyan 500 tare da wasu kasashen Afrika 10 domin yaki da tarin fuka a cikin shekara uku masu zuwa.
Asusun zai kashe dala biliyan 12.7 a kasashe masu tasowa domin yaki da cututtukan kanjamau, tarin fuka da zazzabin cizon sauro.
A dalilin annobar korona akwai yiwuwar samun karuwar akalla mutum miliyan 6.3 da za su kamu da cutar, mutum miliyan 1.4 da za su mutu a dalilin tarin fuka a duniya daga wannan shekaran 2020 zuwa 2025.