An sako kakakin yada labaran hukumar shige-da-fice da mahara suka sace

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta sanar da sako kakakin yada labarai ta hukumar shige-da-fice na jihar Bridget Esene wanda masu garkuwa da mutane suka sace a hanyarta ta zuwa Coci ranar Lahadi.

Kakakin rundunar Chidi Nwabuzor ya bayyana wa manema labari cewa maharan sun sako Bridget da misalin karfe hudu na yammacin Talata.

Nwabuzor ya ce ba shi da masaniyan ko saida aka biya kudin fansa kafin a sako ta ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta baga labarin yadda maharan suka yi garkuwar da Bridget yayin da take hanyar zuwa coci ranar Lahadi ta ta gabata.

Masu garkuwan sun rika bin ta ne tun daga unguwar su da ke cikin babban birnin jihar Edo, su ka ritsa ta a kan hanya, daga nan kuma su ka rika jan ta a kasa, har su ka jefa ta cikin motarsu su ka arce da ita.

Wani jami’in da ya nemi a sakaya sunan sa a lokaci da ake ruwaito sace ma’aikaciyar, ya bayyana cewa an tsinci motar ta a kan hanyar Agbor Road bayan maharan sun yi awon gaba da ita.

Kwannan jami’ar uku tsare a hannun masu garkuwan.

Har yanzu dai ana fama da hare-haren ‘yan bidiga a sassa ban da ban din kasar nan.

A bangaren gwamnati kuma shugaba buhari na cigaba da yi wa bangaren tsaron kasar nan garambawul wanda daga ciki aka sauya manyan hafsosbin kasar nan da sabbi.

Share.

game da Author