Babban Faston cocin darkar Katolika dake jihar Sokoto, Mathew Kukah ya zargi wasu kungiyoyin addinin musulunci da ingiza mabiyansu su afkamasa sannan su ta da zaune tsaye.
Kuka ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar ranar Litinin inda ya ke sukan sakataren kungiyar Jama’atu da Dakta Khalid da yin Kalaman Batanci a garsa da kuma yi masa kazafi a bayanan da yayi ranar kirsimeti.
Dakta Khalid ya soki kalaman Kuka wanda yayi ranar Kirsimet inda ya ke sukar gwamnatin Buhari da nuna fifiko ga yankin Arewa sannan kuma da karrama mususlunci fiye da sauran addinan kasar nan.
A martanin da Kukah ya maida wa Dakta Khalid, ya karyata kalamai da zargin wai yana ruruta wutar tashin hankali tsakanin Kiristoci da Musulman kasar nan. Ya ce duka abin da Dakta Khalid ya ke korafi a aki bai fade su ba. Babu inda ya soki musulunci a jawabin Kirsimeti din.
” Idan akwai inda na soki musulunci a jawabi na na kirsimeti, ina son Dr Khalid ya nuna wa duniya. Ban fadi ba kuma ban taba fadi ba, ko a rubuce-rubuce na ban taba yi akan addinin musulunci ba. Iyakan abinda zan rubuta basu wuce yadda za a samu hadin kan kasa gaba daya.
Idan ba a manta ba tun bayan kalaman da Kukah yayi ranar Kirsimeti, game da mulkin shugaba Buhari, da ikirarin da yayi cewa ana nuna wa musulunci fifiko fiye da sauran addinai da kuma nuna son kai, mutane musamman kungiyoyin musulunci suka rika fitowa suna sukar sa da kuma gargadin sa da kokarin tada zaune tsaye.
Discussion about this post