KORONA: Mai yiwuwa a dage rajistar hada layin waya da lambar katin dan kasa (NIN) – Ministan Lafiya

0

Karamin Ministan Lafiya Olorunnimbe Mamora, ya bayyana cewa ana duba yiwuwar dakatarwa da kuma dage aikin rajistar katin dan kasa saboda ci gaba da barkewar cutar korona.

Dakatarwar inji shi za ta kasance ne ganin yadda ake cinkoso wajen yin rajistar katin, a lokacin da cutar korona ke kara illa a kasar nan.

Mimora ya yi wannan bayani ne a gidan talbijin na Channels, a lokacin da ake wata ganawa da shi a ranar Litinin.

Ministan wanda ya na daya daga cikin mambobin Kwamitin Dakile Cutar Korona na Shugaban Kasa, ya ce, ‘‘abin damuwa ne matuka ganin yadda jama’a ke yin dafifi da cincirindo a dukkan ofisoshi da cibiyoyin Hukumar Katin Dan Kasa ta Najeriya (NIMC).”

“Ba mai jin dadin wannan lamari ko kadan. Ba na jin dadin ganin cincirindon jama’a sun yi irin dafifin da mu ke ganin ana nuno hotunan su.

Ina kuma sane da cewa ita ma Ma’aikatar Sadarwa wadda wannan aiki ke karkashin ta, ta na sane da dukkan abin da ke faruwa.

“Abin da kawai na fahimta shi ne akwai bukatar a dakatar da aikin gaba daya, sannan a sake samun loakcin da za a sake tsarin dungurugun ta hanyar kauce wa yin dafifi a wuri daya. Kamata yay i a ce jama’a na jira, sai an kira sunayen su sannan za su rika zuwa ana yi masu rajistar.”

Share.

game da Author