Ministan ilimi Adamu Adamu ya bayyana cewa ana duba yiwuwar dage ranar komawar dalibai makarantun kasar nan saboda yaduwar Korona da ya tsananta a wannan wata.
Adamu ya fadi haka ne ranar Litini a ganawar kwamitin PTF da manema labarai ranar Litini a Abuja.
Idan ba a manta ba a watan Disamba kwamitin PTF ta bada umurnin a bude makarantun kasar nan ranar 18 ga Janairu domin yara su koma karatu.
Adamu ya ce yanzu da cutar ta sake darkakowa a kasar nan ya zama dole a sake duba yiwuwar bude makarantun saboda kada a saka yara cikin hadari.
Ya ce bayan tattaunawa da kwamitin PTF ma’aikatar ilimi za ta Kara tattaunawa da ma’aikatanta ranar Talata domin tsaida da ranar da ya fi dacewa dalibai su koma makaranta.
Yaduwar cutar korona a Najeriya
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1244 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –774, FCT-125, Filato-102, Anambra-47, Ondo-46, Rivers-27, Edo-18, Kaduna-16, Ogun-16
Gombe-16, Bauchi-11, Kano-11, Nasarawa-10, Akwa Ibom-7, Sokoto-7, Borno-5, Ekiti-4 da Zamfara-2.
Yanzu mutum 101,331 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 80,491 sun warke, 1,361 sun rasu.
A ranar Lahadi, mutum 1024 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Filato, Benue, Zamfara, Rivers da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 36,875, FCT –13,573, Oyo – 4,323, Edo –3,096, Delta –1,982, Rivers 3,940, Kano –2,455, Ogun–2,700, Kaduna –5,817, Katsina -1,687, Ondo –1,990, Borno –835, Gombe –1,456, Bauchi –1,093, Ebonyi –1,147, Filato – 5,783, Enugu –1,455, Abia – 1,086, Imo –801, Jigawa –419, Kwara –1,495, Bayelsa –569, Nasarawa – 1,101, Osun –1,065 , Sokoto –536, Niger – 477, Akwa Ibom – 519, Benue – 601, Adamawa – 497, Anambra –433, Kebbi –223, Zamfara –159, Yobe – 207, Ekiti –443, Taraba- 226, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.