A ranar Lahadi cikin dare gobara tashi a kasuwar Katako mafi girma aAfrika dake Kugbo, Abuja.
An kiyasta cewa shaguna sama da 100 ne suka babbake a kasuwar cike makil da katako. An yi sa a ba a rasa rai ko daya a gobarar domin wutar ta tashi ne a lokacin da ‘yan kasuwa sun tashi sun koma gida.
‘Yan kasuwan sun ce wannan shine karo na uku da kasuwar ke babbakewa saidai ba kamr wannan gobarar da aka yi ranar Litinin.
Da yake tattaunawa da wakillin PREMIUM TIMES ranar Litini Jude Okeke ya ce yayi asaran kayan akalla naira miliyan 15.
” Ina da ‘ya’ya uku banda wasu hidimomin rayuwa na yau da kullum. Idan ba ikon Allah ba bubu yadda za a yi na ci gaba da wannan sana’a.
Ann Chinelo ta ce wannan shine karo na uku da kasuwar ke babbake wa.
Osas Williams ya ce bai yadda cewa jarabawa ce ya fado musu ba a wannan kasuwa.
Ya ce yana ganin akwai wadanda suke wa kasuwar hassada suka biyo dare suka cinna mata wuta don kowa ya samu karayar arziki.
Akwai wadanda suka ce sun yi asarar dukiya har na sama da miliyan 50 a shagunan su.
A karshe ‘yan kasuwan sun yi kira ga gwamnati ta kawo musu dauki, domin dayawa wasu kuma shikenan sun fada cikin karayar arziki kenan har abada.