Za a bude makarantu a jihar Bauchi ranar 18 ga Janairu

0

Gwamnatin jihar Bauchi za ta bude makarantun jihar 4,816 ranar 18 ga Janairu.

Kwamishinan ilimin jihar Aliyu Tilde ya Sanar da haka a garin Bauchi ranar Talata.

Wannan sanarwa ya fito adaidai gwamnatin tarayya na duba yiwuwar dage ranar komawa makarantun kasar nan saboda fantsamar da Korona ta yi a fadin Najeriya da ya sa a kusan kullum mutum sama da Dubu ke kamuwa a kasar.

Tilde ya ce makarantun da za a bude za su fara karatun zangon farko na shekaran 2020/2021 wanda bisa ga tsari ya kamata a fara tun a watan Satumbar 2020, amma ba a samu daman yin haka ba saboda Korona.

Ya ce kowace makaranta za ta tabbata ta kiyaye dokokin Korona sannan kuma Tilde ya kara da cewa tuni gwamnati ta yi feshi a duka makarantun jihar domin kashe cututtuka.

“Za a hukunta duk makarantar da aka samu tana sabawa dokokin Korona.

Tilde ya yi kira ga iyaye da su shirya ‘ya’yan su domin za a fara karatu ranar 18 ga Janairu.

A ranar 11 ga Janairu PREMIUM TIMES ta buga labarin sbirin gwamnatin tarayya na dage ranar komawar dalibai makarantu saboda ci gaba da cutar korona.

Ministan ilimi Adamu Adamu ya ce ya zama dole a sake duba ranar da dalibai za su koma makaranta a kasar nan.

Ya ce bayan tattaunawa da kwamitin PTF ma’aikatar ilimi za ta Kara tattaunawa da ma’aikatantar ranar Talata domin tsayar da ranar da ya fi dacewa dalibai su koma makaranta.

Share.

game da Author