Gwamnatin Tarayya ta amince a kashe naira milyan 204 wajen bude shafin fasahar intanet domin sa-ido kan ayyukan manyan titinan kasar nan.
An amince da kashe kudaden domin kwangilar tsara manhajar fasahar ICT ta zamani da za a rika kula da ayyukan kwangilolin kan titina da kuma kula da titinan su kan su daga saurin lalacewa da su ke yi.
Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ne ya bayyana haka a ranar Laraba, bayan fitowar su daga Taron Majalisar Zartaswa, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.
A wannan taro na 31 ne da aka gudanar a ranar Laraba, aka amince a bayar da kwangilar aikin ta naira milyan 203,845,333.50.
Ya ce wannan fasaha za ta samar da tsari na kula da ayyukan titi da kuma ingancin ayyukan su kan su.
Fashola ya ce manyan titinan gwamnatin tarayya sun yi tsawo da yawan da wani titin ma kamata ya yi a ce ‘yan kwangila biyar ne aka ba aikin sa.
Sai yace wannan sabon shafin manhajar fasahar zamani ta ICT, zai zama kamar wani tabaran hangen nesan da gwamnatin tarayya za ta rika kula da ayyukan da da kuma sa ido kan titinnan.
“Wannan tsari kuma zai taimaka wajen sauri da gaggawar gyara wuraren da titinan gwamnatin tarayya su ka lalace.
“Zai kuma karfafa masu kula da shi har mutum 36 a kowace jiha, tare da daraktocin shiyya su shida.” Haka Fashola ya shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, jim kadan bayan tashi daga taro.
“Za a kara fahimtar muhimmancin wannan sabon tsarin kula da ayyukan kwangilolin manyan titinan gwamnatin tarayya, idan aka yi la’akari da cewa ya zuwa watan Disamba, 2020, aikin titin gwamnatin tarayya da ake ci gaba da yi a fadin kasar nan ya kai na kilomita 13,000 a jimlace.”
Ya ce kuma an bayar da aikin ga kwangila daban-daban da ta kai har guda sama da 700.
“Misali kun ga kamfanin kwangila biyar ne ke aiki a kan titin Kano zuwa Maiduguri, kowanen su a wurare daban-daban, saboda tsawon titin. Haka titin Benin zuwa Lokoja ma akwai kamfanonin kwangila biyar a kan sa.” Cewar Fashola.