Asusun Najeriya na kasar waje ya karu da ribar danyen mai ta dala bilyan 1.3

0

Babban Bankin Najeriya, CBN ya bayyana cewa Asusun Kudaden Kasashen Wajen Najeriya da ke waje ya samu karin ribar kudaden danyen man fetur har ta dala bilyan 1.3 a cikin watan Nuwamba na shekarar 2020.

Wato ya zuwa watan Janairu, 2021, asusun ya tashi daga dala bilyan 34.94 a cikin Nuwamba, ya koma dala bilyan 36.23 kenan a cikin Janairu, 2021.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefile ne ya bayyana haka a taron Kwamitin Tsara Tasarifin Kudaden Najeriya na bankin CBN da aka gudanar a ranar Talata.

Ya ce karin kudaden da asusun na Najeriya ya samu ya dogara ne da irin kudaden shigar da kasar nan ta samu daga man fetur.

“Kwamitin MPC ya lura da karin kudaden da Asusun Najeriya na Kasashen Waje ya samu, inda kudaden da ke asusun su ka karu daga dala bilyan 36.23 ya zuwa ranar 21 da Janairu, 2021, idan aka yi la’akari da yadda asusun ya ke cike da dala bilyan 34.94 a karshen watan Nuwamba, 2020.” Inji Emefile.

“Karin ya samu ne daga kudaden danyen fetur da mu ka samu sanadiyyar farfadowar da tattalin arzikin duniya ya fara yi.

“Wannan farfadowa kuwa ta samu asali ko sanadi ne daga fara samun allurar rigakafin cutar korona da aka fara yi a fadin duniya, musamman daga kasashen masu karfin tattalin arziki.”

Daga nan ya kara da cewa a yanzu za a iya cewa tattalin arzikin Najeriya da na duniya ya fara farfadowa tare da samun tagomashi, saboda hobbasan da duniya ta yi wajen samun rigakafin korona.

Ya ce sai ma karshen watan Maris na 2021 za a fara ganin tagomashin karin farfadowar tattalin arzikin Najeriya sosai da sosai.

Daga nan sai Gwamnan CBN din ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara daukar kwararar matakan samar da tsaro, kawar da kalubaen da matsalar tsaro ke haifa wa kasa, tare da dakile tsadar rayuwa da kuncin matsi ga talakawa sakamakon tsadar kayan abinci.

Emefile da sauran ‘yan kwamitin sun ce matsalar tsaro da tsadar kayan abinci na ci gaba da yin barazana a kasa nan, ta yadda idan ba a kawar da su ba, to ko tattalin arziki ya farfado, ba lallai ba ne a ji a jika har ya yi tasiri a cikin al’umma ba.

Share.

game da Author