Duk da dawowar Korona gadan-gadan, gwamnati ta amince dalibai su koma makaranta ranar 18 ga Janairu

0

Ministan Ilimi Adamu Adamu ya bayyana cewa gwamnati ta amince da bude makarantu ranar 18 ga Janairu domin uara su koma makaranta.

Jami’n hulda jama’a na ma’aikatar Ben Goog ya tabbatar da haka a wata takarda da ma’aikatar ta fitar ranar Alhamis.

Goog ya ce sai da aka yi nazari mai zurfin gaske kafin aka amince yara su koma makaranta kawai.

” Ma’aikatar ta yi zaman musamman da gwamnoni, kwamishinonin Ilimi, kungiyoyi, malamai da masu makarantu kafin dukkan su suka cimma wannan matsaya.”

Ma’aikatar ta ce dole makarantu su kiyaye bin dokokin kare kai daga Korona tunda wuri ta hanyar samar da ruwan wanke hannu da man tsaftace hannu.

Sannan kuma a daina yin asambili, da duk wani taro da zai sa yara su gwamutsu wuri daya.

Kuma kowani yaro zai saka takunkumin fuska a koda yaushe sannan a rage cinkoson yara a ajujuwa.

Share.

game da Author