Kodinaton Kwamitin Shugaban Kasa Kan Dakile yaɗuwar Korona, ta gargadi mutane su daina yaɗa maganganun da ba a yi su ba don tada hankulan mutane musamman game da Korona.
Idan ba a manta ba an rika yaɗa labarai cewa wai gwamnatin tarayya za ta sake garkame kasa saboda darkakowar da Korona ta yi. Saidai Sani Aliyu ya ce wannan magana babu gaskiya a cikin sa.
” Kwamitin shugaban kasa bata taɓa fidda wata sanarwa cewa wai zata sake maida mutane cikin ‘Kulle’ a Najeriya ba. Duk labaran kanzon kurege ne ake yadawa.
Aliyu ya gargadi mutane da su daina yada ire-iren wadannan maganganu da basu da tushe.
” Mu dai a kwamitin mu ba a taɓa kawo wannan magana ba, wasu ne kawai da ke neman kawo ruɗani a tsakanin mutane suke yaɗa karairayi irin haka, su shiga taitayin su tunda wuri, sannan su daina haka.
Makonni biyu kenan a jera ana samun mutane sama da dubu a kullum da suke kamuwa da Korona a kasarnan.
Sai dai hakan bai sa mutane sun shiga taitayin su ba wajen kiyaye dokokin kamuwa da cutar, wato ta hanyar saka takunkumin fuska, wanke hannaye da daina gwamatsuwa ba.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin sanarwar ma’aikatar Ilimi na amincewa a bude makarantu ranar 18 ga Janairu.
Ministan Ilimi Adamu Adamu, ta bakin kakakin ma’aikatar Ben Goog, ya ce za bude makarantu ranar 18 Janairu kamar yadda ma’aikatar ta sanar a farkon wannan watan.
Discussion about this post