KORONA: An samu karin mutum 1,479 da suka kamu ranar Alhamis

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1479 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –697, FCT-201, Nasarawa-80, Filato-74, Rivers-72, Edo-46, Adamawa-43, Osun-39, Akwa Ibom-35, Delta-31, Anambra-27, Oyo-24, Kano-21, Abia-19, Enugu-19, Ogun-18, Sokoto-12, Bauchi-7, Taraba-7, Ekiti-4, Gombe-4, Imo-4, Bayelsa-2, Jigawa-2 da Zamfara-1.

Yanzu mutum 105,478 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 83,830 sun warke, 1,405 sun rasu.Sannan zuwa yanzu mutum 20,253 ke dauke da cutar a Najeriya.

A ranar Laraba, mutum 1398 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Filato, Oyo, Rivers, Kaduna da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 38,549, FCT –14,139, Oyo – 4,570, Edo –3,189, Delta –2,062, Rivers 4,186, Kano –2,512, Ogun–2,745, Kaduna –5,888, Katsina -1,692, Ondo –2,006, Borno –844, Gombe –1,471, Bauchi –1,107, Ebonyi –1,159, Filato – 6,147, Enugu –1,525, Abia – 1,114, Imo –810, Jigawa –423, Kwara –1,566, Bayelsa –588, Nasarawa –1,233, Osun –1,149, Sokoto –602, Niger – 508, Akwa Ibom – 588, Benue – 629, Adamawa – 540, Anambra –460, Kebbi –240, Zamfara –160, Yobe – 207, Ekiti –450, Taraba- 246, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.

Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya gargadi masu yada labaran karya game da Korona da su shiga taitayin su cewa duk wanda aka samu yana haka zai dandana kudan sa.

“ Ina gargadin masu yada labaran ƙarerayi game da Korona da su daina domin ni kaina na kama wannan cuta kuma na san irin bakar wahalar da na sha kafin na warke daga cutar.

Ya ce duk wanda aka kama zai dandana kudar sa.

Bayan haka gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda mutane suka yi watsi da bin dokokin Korona a jihar.

Ya ce hakan ya zama abin damuwa a gare sa musamman yadda mutane ke kara kamuwa da cutar kuma ana ta samun karuwar wadanda ke mutuwa.

Lalong ya ce ya zama dole a ci gaba da wayar da kan mutane game da cutar da hanyoyin da za su bi don kiyaye ka su.

Maganin rigakafi

Lalong ya kuma gargaddi mutanen jihar da su nisanta kansu daga yada labaran karya game da maganin rigakafin cutar.

Ya ce a yanzu haka masana kimiya da masana kimiyyar magunguna na jihar na kokarin hada maganin rigakafin cutar a jihar wanda hukumomin kula da inganci da sahihanci magani za su tabbatar da ingancin maganin.

Share.

game da Author