Daga zata ganin gida, ban sake ganin matata ba – Inji Malam Sani a Kotu

0

Wani magidanci mai suna Sanni Alimi ya kai kara a raba auren sa da matarsa cewa shekarar sa hudu kenan bai saka ta a Ido.

Sani ya shaida wa kotu cewa matarsa ta roke shi za ta ganin gida. ” Yau shekara hudu kenan ban saka ta a ido ba. Da na nemi mahaifiyarta ta yi min bayani, sai ta ce min wai lallai matata ta zo gida amma ta koma Legas gidan wata ‘yar uwar ta.

” Da muka ci gaba da binciken inda take sai muka gano ashe sun hada baki da mahaifiyarta ne ta gudu zuwa kasashen waje.
Daga nan sai ya ce ya gaji da kwallo da shi da ake yi, ya roki kotu ta raba auren su kawai duk inda ta tafi ma idan ta dawo ta kama gaban ta.

Shi ko Alkalin kotun bai yi wata-wata, bayan saurarenta ya warware kullin auren. Ya ce Malam Sanni ya kama gaban sa kawai ya ce yayi aure. Idan ta dawo ya rage nata da uwar.

Share.

game da Author