Wani magidanci ya shigar da kara kotu a Ibadan yana neman kotu ta raba aurensa da matar sa dalilin gano cewa ta na yi masa asiri don ta mallaki dukiyar sa.
Mista Kolawole mijin Olubunmi, na aiki a wani kamfani dake Ibadan kuma yana da wasu matan guda biyu.
Kolawole ya gano ashe tuntuni a tsawon zaman su, matarsa tana amfani da asiri ne tana juya shi yadda take so. Ya gano haka ne bayan ya samu wani tattaunawarta da bokan da ke yi mata tsubbace-tsubbacen da aka dauka a waya.
A wannan tattaunawa Kolawole ya ji karara cewa matarsa ta yanke hukuncin kawai a hada surkullen da zai sha ya fada cikin yanayi na ciwon da ba zai taba warkewa ba, wanda a karshe kawai ma ya mutu a huta.
Ta na cewa a cikin wannan hira ta da boka, tana so ya dan wahala ne tukuna da ciwo mai tsanani kafin ya sheka lahira, ita kuma ta gama shiri tsaf yadda za ta kwashe abin da ya mallaka ta kama gabanta sauran matan kuma ko oho.
Da alkali ya saurari wannan hira da aka dauka, sai ya umarci matar Kolawole ta ce wani abu akai, wato ta kare kanta.
Sai dai kuma jin wannan hira da aka dauka tsakanin ta da boka ya kashe mata jiki, sai kawai ta amsa laifin ta.
Tace ” A gaskiya na rika yayyafa wa mijina tsafe-tsafe ne domin in mallake shi kuma in mallaki dukiyar sa. lallai na yi haka sai dai saboda tsananin kishin amaryarsa ne yasa nayi haka.
A karshe Alkalin kotun ya raba auren, kuma ya mika wa matar ‘yayan su ta ci gaba da kula da su har su girma. Shi kKlawole zai rika bata naira 6000 duk wata domin kula da yaran.