Sauya fasalin Najeriya kadai ba zai magance matsalolin mu ba – Jonathan

0

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ko an sauya fasalin Najeriya, ba za a iya magance matsalolin da su ka dabaibaye kasar ba.

Jonathan ya ce magance matsalolin kasar nan sai an magance bambance-bambancen da su ka raba kasar tukunna.

Haka tsohon shugaban kasar, wanda ya yi mulki tsakanin 2010 zuwa 2015 ya bayyana a taron shekara-shekara da jaridar Daily Trust ke shiryawa.

An gudanar da taron na 18 a ranar Alhamis.

Jonathan ya nuna matukar damuwar sa kan yadda bambanci da bangaranci ya yi katutu a cikin siyasar Najeriya.

Ya ce wannan ya na sahun gaba daga cikin sabubban da su ka tauye Najeriya, su ka hana kasar matsawa domin ci gaba.

Ya ce ba laifi ba ne don an sauya fasalin kasa, amma tilas tsarin ba zai yi tasiri ba, sai idan ya tafi kafada-da-kafada da kaunar juna da kuma hadin kai a cikin kasa baki daya, musamman a samu shugabannin da za su iya tabbatar da wannan hadin kai.

Ya bada shawarar ko za canja fasalin kasa, to kada ya kasance an yi tsarin bisa turba ko amfani da shata kan iyakokin addini ko ta bambancin kabilu.

Sannan ya kara da cewa matsaloli da kalubalen da kasar nan ke fuskanta, ba wai a tarayya kadai ba, har a jihohi da kananan hukumomi ana ganin su kuru-kuru.

Don haka ne ya ce ba wai sauya fasalin kasa ne kadai zai iya magance matsalolin ba.

Jonathan ya ce sai an sauya fahimta da tunanin da ake yi wa juna a lamarin zamantakewar al’umma mabambanta a cikin kasa daya.

“Ba za mu iya sauya fasalin Najeriya ba tare da magance matsalolin da su ka dabaibaye mu ba tukunna.

“Mu na fama da kabilanci, bangaranci, bambancin addini da na dabi’u da kuma tantagaryar rashin kishin kasa.” Cewar Jonathan a wurin taron.

“Wannan batu abu ne mafi muhimmanci da ya ceci Najeriya daga tarwatsewa bayan Yakin Basasa.

“Ya zama wajibi mu yi iyakar kokarin mu ko daga ina mutum ya ke zaune, domin mu magance kalubalen da ke tattar da mu. Sannan kuma mu yi aiki tukuru domin maida Najeriya kasaitacciyar kasar da nan gaba ‘ya’yan mu za su ci moriyar ta tare kuma da yin alfahari da ita.

Sai dai kuma ya ce duk ba za a iya kaiwa ga wadannan nasarori ba, sai an dabbaka kaunar juna da hadin kai a cikin kasar baki daya.

A wurin taron da wasu da su ka yi jawabi sun amince da shawarar Jonathan. Amma wasu sun bada na su shawarwari daban.

Cikin wadanda su ka ki amincewa da bayanan Jonathan, har da tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa, Attahiru Jega, wanda a karon farko su ka hadu ido-da-ido da Jonathan, tun bayan zaben 2015, wana Jonathan din bai yi nasara ba.

Share.

game da Author