Yawancin almajiran Arewa ƴan Nijar, Kamaru da Chadi ne – Ganduje

0

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya yi ikirarin cewa yawancin almajiran da ke gararamba kan titinan Arewa, ƴan asalin kasashen da ke makwabtaka da Najeriya ne.

“Akasarin almajiran da alr gani su na gararamba kan titin mu, ba ‘yan Najeriya ba ne, ‘yan Nijar da Kamaru da Chadi ne. Daga can ake turo su almajirci garuruwan mu.”

Haka Ganduje ya bayyana a lokacin da ya ke bude taron kwana uku na Hukumar Bayar da Ilmi a Matakan Farko (UBEC) a Kano.
Ganduje ya bude taron a ranar Litinin.

“Daga wani bincike da muka gudanar da kididdigar almajiran da ke gararamba kan titina da garuruwan Arewa, Akasarin su daga Nijar, Chadi da Arewacin Kamaru su ka fantsamo nan Arewa.”

“Najeriya mashiga ce kuma mafita daga kasashen Afrika ta yamma.

“Babbar matsalar da mu ke fuskanta ita ce, idan ka inganta rayuwar almajirai yau, to gobe kuma sai ka ga wasu sun kara tudadowa.

“Amma dai Gwamnonin Arewa na nan na kokarin kafa dokar-bai-daya, wadda za ta hana karakainar almajirci daga wannan jiha zuwa waccan.”

Ganduje ya ce taron sanin makamar ya na da muhimmanci, musamman a wannan lokaci daidai da fita daga kuncin korona, cutar da ta yi wa harkokin ilmi illa sosai a Najeriya.

Ya ce akwai matukar muhimmanci ga taron “kasancewa ana gudanar da shi ne daidai lokacin da yawan yaran da ake haihuwa sun fi nauyin aljihun kudaden da ake iya kashewa a bangaren ilmi a kasar nan.”

Babban Sakataren Hukumar UBEC, Hamid Bobboyi, ya ce makasudin taron shi ne domin a yamutsa gashin baki, a lalubo hanyoyin da za a ciyar da ilmi gaba, a bunkasa shi.

Share.

game da Author