Shahararren dan wasan kwallon kafa na Juventus wanda kuma ya shahara wajen jefa kwallaye a ragar abokan karawa, ya lallasa Barcelona a filin su, Camp Nou a wasan karshe na rukunin guruf G.
Barcelona ce ta karbi bakuntar Juventus daga kasar Italy.
Abu kamar wasa dai, sai da Juventus ta jefa kwallaye 3 a ragar Barcelona ita kuma Barcelona ba ta iya jefa koda kwallo daya bane.
Ronaldo ya zura kwallo biyu a ragar Barcelona duk da Messi da suke da shi.
A karshe dai Juventus ce ta yi nasara a wasan sannan kuma itace ta zo daya a rukunin su.
Discussion about this post