RIKICIN APC: Nasiha da gargadin da Buhari ya yi wa Shugabannin Jam’iyya

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga shuhabannin jam’iyyar APC na kasa su daure, su jajirce su dauki damarar yin aikin sadaukarwa ga jam’iyyar APC domin samar da hadin kai.

Buhari ya yi wannan jawabi a ranar Talata, wurin taron shugabannin zartaswa na APC a Abuja.

“Ina yin kira ha shugabanni da mambobin jam’iyya baki daya a daure, a jajirce a sadaukar da kai wajen dawo wa APC da martabar ta da kyawawan ka’idun dimokradiyyar da aka san ta da su.

” Ta haka ne dukkan fata da muradin da muka yi na kokarin gina inganyacciyar Najeriya zai tabbata.”

Taron ya samu halartar Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila, Gwamnoni da sauran shugabannin APC.

Buhari ya jinjina wa jagorancin watanni shida da Gwamna Mala Buni ya yi ya na rikon APC, inda ya ce shugaban na riko ya cancanci jinjina da yabo matuka.

Buhari ya ce duk da rikita-rikitar da ta dabaibaye APC, sai ga shi jam’iyyar ba ta samun matsalar masu fita su na komawa PDP. Maimakon haka, manyan PDP ne ma ke komawa APC.

Daga nan ya yaba wa masu komawa APC daga PDP, musamman Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi.

Buhari ya ce ya zama tilas a sabunta rajistar ‘yan jam’iyya a kasar nan baki daya.

Ya kuma yi fatan samun shugabanni managarta tun daga tarayya, jihohi da kananan hukumomi wadanda za su iya rike ragama da linzamim jam’iyya, riko na kwarai, ba rikon-sakainar-kashi ba.

Share.

game da Author