Gwamnatin Tarayya ta dibi karin Talakawa 32,236 da za su rika samun tallafin naira N5000 duk wata a Kaduna

0

Gwamnatin Tarayya karkashin shirinta na Conditional Cash Transfer (CCT) ta kara diban talakawa sama da 32,000 domin basu kudaden tallafi duk wata a jihar Kaduna.

Gwamnati ta kirkiro wannan shiri domin tallafa wa talakawa da kudin cin abinci kai tsaye duk wata.

Shugaban wannan hukuma ya CCT ta bayyana a garin Kaduna, a lokacin da take hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa dama can akwai mutum 34, 946 da suke cin moriyar wannan shiri da suka fito daga kananan hukumomin Birnin Gwari, Chikun, Ikara, Kachia, Kauru, Kubau, Lere, Kajuru da Sanga.

A wannan daukan an dibi jama’ar kananan hukumomin Giwa, Igabi, Jaba, Kaduna Ta Arewa, Kaduna Ta Kudu, Kagarko, Kaura, Kudan, Makarfi, Sabon Gari, Soba, Zangon Kataf, Zaria, da Jema’a.

A karkashin wannan shiri na CCT, za a rika ba kowani talaka naira N5000 duk wata domin ya rika samun abin da zai saka a bakin salati.

Zuwa yanzu a karkashin wannan shiri akwai talakawa sama da 200,000 da aka tantace a rajistar hukumar a jihar Kaduna.

Share.

game da Author