MARTANIN APC GA KWANKWASO: Za mu maimaita ‘Inkonkulusib’ ba ma a Kano ba har a Najeriya

0

Shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya, Abdullahi Abbas ya bayyana cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso bai isa ya hana jam’iyyar yin abinda ta ga dama a zaben Kano ba a 2023.

” Za mu yi abinda muka ga dama a zaben 2023, kamar yadda muka yi a Gama, a 2019. Haka za mu yi har ma da kasa baki daya, Kwankwaso bai isa ya hana mu ba.

Wadannan sune irin kalaman da shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC a jihar Kano Abdullahi Abbas yayi a wajen rantsar da shi da aka yi a Kano.

Bayan nan ya kara da cewa idan Kwankwaso ya cika dan siyasa, ya sa ‘ya’yan sa a gaba a lokacin kamfen idan aka buga gangar siyasa a 2023.

” ‘Ya’yan sa duk suna Dubai ya boye su, ya na na yana cika baki na wasu su fito. Yayi yadda muke yi, ba wai ka boye naka ba ka saka na wasu a gaba. Ko zabe ba zai fito yayi ba, karyan banza yake yi ba zai fito ba.

A karshe, Abbas ya yi kira ga magoya bayan su su aikata wa duk wanda ya zagi gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ko kuma jam’iyyar APC a Kano.” Kada ku ji komai, mu ne a gwamnati yanzu sai yadda muka so.

Share.

game da Author