Hukumar SSS ta yi gargadin yiwuwar tada bom da hare-haren ta’addanci lokacin Kirsimeti da sabuwar shekara

0

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) ta yi gargadin cewa jama’a su yi kaffa-kaffa, domin akwai yiwuwar hare-haren tayar da bom da sauran harin ta’addanci a lokutan bukukuwan Kirsimeti a Najeriya.

Cikin wata sanarwa da Kakakin SSS, Peter Afunaya ya fitar ga manema labarai a ranar Talata, an yi gargadin cewa a yi kaffa-kaffa da shiga cikin rintsin tarukan jama’a, domin masu tayar da bom, sun fi tunkarar inda gungun jama’a su ka yi dafifi.

Afunanya ya ce hare-haren wasu marasa kishi ne ke shirya shi domin su kawo wa gwamnatin tarayya kafar-ungulu.

Ya yi kira ga jama’a su ka rahoto ga jami’an tsaro na wani ko wasu mutane bakin-idon da ba su yarda da su ba.

Ya ce ana hasashen kai hare-haren na bom da hare-haren kunar-bakin-wake ne a wasu wuraren da ake ganin babu wadattacen tsaro, domin a yi wa gwamnatin tarayya kafar-ungulu.

A bangaren SSS, Afunanya ya ce hukumar na aiki kafada da kafada da sauran bangarorin tsaro domin su tabbatar da tsaron rayuka da dunkiyoyin jama’a.

Domin kara inganatawa da karfafa matakan tsaro, SSS ta fitar da lambobin wayoyin a za a kira domin tuntubar gaggawa.

Lambobin kamar yadda Afunanya ya fitar, su ne: *08132222105* da kuma *09030002189*.

Akwai kuma shafin intanet na www.dss.gov.ng wanda za a iya shiga domin karin bayanan da duk ake bukata.

Yayin da Hukumar SSS ke jan kunnen duk masu neman haddasa fitina su kuka da kan su, kada a damke su, Afunanya ya kara da cewa hukumar a karkashin Babban Daraktan ta Y. Bichi na yi wa al’ummar Najeriya murna da fatan gudanar da bukukuwan Kirsimeti lami lafiya.

Share.

game da Author