Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 999 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –324, FCT 416, Kaduna 68, Filato 42, Kwara 32, Kano 24, Gombe 14, Sokoto 12, Yobe 12, Akwa Ibom 11, Bayelsa 10, Rivers 7, Bauchi 7, Ogun 6, Oyo 5, Edo 4, Taraba 4 da Jigawa 1.
Yanzu mutum 79,789 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 68,879 sun warke, 1,231 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 9,679 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Litini, mutum 356 suka kamu a Najeriya, jihohin Kaduna, Legas, Katsina da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 27,091, FCT –10,122, Oyo – 3,793, Edo –2,790, Delta –1,843, Rivers 3,293, Kano –2,081, Ogun–2,389, Kaduna –4,628, Katsina -1,442, Ondo –1,793, Borno –778, Gombe –1,192, Bauchi –904, Ebonyi –1,091, Filato – 4,304, Enugu –1,376, Abia – 983, Imo –734, Jigawa –387, Kwara –1,328, Bayelsa –507, Nasarawa –630, Osun –979, Sokoto – 247, Niger – 381, Akwa Ibom – 413, Benue – 515, Adamawa – 355, Anambra – 299, Kebbi – 155, Zamfara – 79, Yobe – 176, Ekiti –405, Taraba- 207, Kogi – 5, da Cross Rivers – 94.
Bayan haka a watan Satumba Kasar Birtaniya ta sanar da bayyanar wata sabuwar samfurin Korona da take mamaye mutanen kasar sannan ana samun karin mutanen kasar da ke ta mutuwa babu kakkautawa.
Masana kuma likitoci masu bincike a cibiyar ACEGID, na jami’ar Redeemers dake jihar Osun.
Ita dai wannan nau’i na Korona mai suna “lineage B.1.1.7” ta bayyana da zafi a kasar Birtaniya, da yasa dole gwamnatin kasar ta saka sabbin dokoki na kiyaye yaduwarta da suka hada da dokar shiga da fice da balaguro a fadin kasar.
Farfesa Christian Happi, ya ce an gano wannan nau’i na Korona ne a gwajin jinin wasu mutum biyu da aka yi wa gwajin Korona. Daga nan ne aka gano cewa tasu Koronan sabuwa ce ba ta da din bace.
Sai dai kuma ba a tabbatar cewa ko wannan nau’i na korona ce yasa ake ta samun karuwar yawan wadanda suke kamuwa da cutar akasar nan yanzu.
Farfesa Happi ya bayyana wa PREMIUM TIMES a hira da yayi ta ita cewa ba zai iya battabar da ko sabuwar Koronar bace take yaduwa kamar wutar daji a kasar nan saboda an gano ta tun a watan Oktoba ne, wanda a lokacin ba a samu yaduwar ba kamar yadda ake samu yanzu.
” Yanzu dai akwai yiwuwar kila a samu karin wadanda suka kamu da cutar ta sanadiyyar wannan sabon nau’i na Korona. Amma dai sai an yi gwaje-gwaje tukunna.
Shugaban hukumar NCDC Chikwe Iheakweazu ya bayyana cewa a yanzu dai suna jiran shawarar hukumar kiwon lafiya ta Duniya, WHO game da wannan nau’i na Korona. Sannan kuma da maida hankali wajen ganin an ci gaba da kiyaye dokokin korona musamman ga matafiya da kuma mutane baki daya.
Sannan kuma, gwamnati ta yi kira ga mutane ci gaba da bin dokokin samar da kariya daga kamuwa da cutar sannan ta hanyar saka takunkumin fuska, yin nesa-nesa da juna da kuma kula da lafiyar jiki.