Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta janye yajin aiki

0

Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU) ta janye yajin aikin da ta ke yi tsawon watanni 10, tun a ranar 9 Ga Maris.

Ta fara yajin aikin ne sanadiyyar tankiya da rashin cika alkawarin da gwamnatin tarayya ta yi na gyara jami’o’i, sai kuma rike wa wasu malaman albashi da aka yi tsawon watanni da dama sakamakon kin yin nrajistar da tasrin biyan albashi na IPPIS.

ASUU ta ce ta janye yajin aikin, amma za ta zuba ido ta ga yadda gwamnati za ta biya masu bukatun da ta amince a bisa sabbin sharudda da yarjejeniyar da ita gwamnain ta amince za ta yi aiki da ita.

Da ya ke magana a Sakatariyar ASUU da ke Abuja ranar Laraba, shugaban kungiyar Biodun Ogunyemi ya ce an janye yajin aikin bayan majalisar zartarwar kungiyar ta yi taro a ranar Talata.

Daga nan ya ce a yanzu dai an sasanta batun tirka-tirkar rajistar tsarin IPPIS tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU.

Da aka tambaye shi yaushe daibai za su koma jami’o’i, ganin cewa cutar korona ta dawo gadan-gadan, sai Biodun ya ce ASUU a shirye ta ke a koma karatu, matsawar dai gwamnati ta samar da matakai na kariya daga cutar a kowace jami’a ta kasar nan.

An shafe watanni tara cur ana tankiya da ASUU da kuma Gwamnatin Tarayya, har ta kai cikin Nuwamba gwamnati ta kama hanyar yi wa Kungiyar Malaman Jam’i’o’i ta Kasa (ASUU) kishiya.

Yayin da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ke ci gaba da yajin aiki tsawon watanni 10, ita kuma gwamnatin tarayya ta fara yi wa wata sabuwar kungiyar malaman jami’o’i rajista.

Ministan Kwadago da Ma’aikata, Chris Ngige ne ya bayyana haka ranar Alhamis a Abuja.

Ya yi bayanin ne a lokacin da shugabannin sabuwar kungiyar, mai suna ‘Congress of University Academics (CONUA) su ka kai masa ziyara.

CONUA ta kai ziyarar ce a karkashin jaforan ta Niyi Sunmonu.

An tattaro malaman jami’o’i na fadin kasar nan ne daga cikin malaman jami’o’in da ba su goyon bayan ASUU.

Ngige ya jajanta a kan yadda ASUU ke ci gaba da yajin aiki, tsawon watanni 10, ya na mai cewa hakan ya maida harkar ilmi baya sosai a kasar nan.

“Mu na murna da wannan ziyara da ku ka kawo a wannan ma’aikata. Domin mu na da iznin karbar bakuncin kowace kungiya, mai rajista ko wadda ba ta da rajista. Ku na da dama da ‘yancin da za ku nemi rajista, domin yin hakan, abu ne mai kyau.” Inji Ngige.

“Mu na da ‘yancin yin taron ganawa da ku. Saboda haka har ma mun fara shirye-shiryen yi maku rajista.

“Kun yi daidai da ku ka nemi a yi wa wannan sabuwar kungiya ta ku rajista. Wannan ma’aikata kuma ta yi daidai da ta fara bin matakan yi maku rajista.

“Na kafa kwamitin bin diddigin matakan yi maku rajista, yanzu kuma zan ce wa kwamitin ya hanzarta kammala nazarin takardun ku domin a yi maku rajistar da gaggawa.” Inji Ngige.

Ya kara da cewa an bai wa kwamitin makonni hudu ya kammala tsare-tsaren sa.

“Dama mu aikin mu a nan ya hada har da yi wa kungiyoyi rajista. Kuma aikin mu ne ganin cewa kungiyoyin da ba su aiki sun samu taimako daga wannan ma’aikata.

Tun farko jagoran kungiyar Sunmonu ya shaida wa Ngige cewa malaman jami’a daban-daban sai tururuwa su ke yi su na shiga sabuwar kungiyar, tun bayan kara ta a watan Fabrairu, 2018.

Ya ce sun kafa CONUA saboda sabani da bambanci tsakanin su ASUU ya ki ci, ya ki cinyewa.

Asalin Yajin Aikin ASUU A Maris, 2020:

Kungiyar Malaman jami’o’i ta Najeiya ta fara yajin aiki na gama gari na makonni biyu a rashin kin biyan wasu daga cikin malaman jami’o’i albashi.

Shugaban kungiyar Biodun Ogunyemi ya bayyana haka bayan ganawar gaggawa da kungiyar ta yi a garin Enugu

Wannan yajin aiki na kwankwasa kyaure ne tukunna, idan gwamnati bata ce uffan ba za su fara yajin aikin gadan-gadan har sai an biya musu bukatunsu.

Daya daga cikin abin da suke kuka da shi ne dagewa da gwamnati tayi sai dole malamai sun yi rajista da shirin biyan albashi na IPPPIS kafin a biya mutum albashi. Daya wa daga cikin malaman jami’oin ba su karbi albashin su ba saboda ba su cikin shirin.

Kungiyar malaman jami’oin kasar nan sun fara yajin aiki na gama gari na makonni biyu a rashin kin biyan wasu daga cikin malaman jami’o’i albashi.

Shugaban kungiyar Biodun Ogunyemi ya bayyaa haka bayan ganawar gaggawa da kungiyar ta yi a garin Enugu.

Wannan yajin aiki na kwankwasa kyaure ne tukunna, idan gwamnati bata ce uffan ba za su fara yajin aikin gadan-gadan har sai an biya musu bukatun su.

Daya daga cikin abin da suke ku ka da shi ne dagewa da gwamnati tayi sai dole malamai sun yi rajista da shirin biyan albashi na IPPPIS kafina biya mutum albashi. Daya wa daga cikin malaman jami’o’in ba su karbi albashin su ba saboda ba su cikin shirin.

Share.

game da Author