KORONA: An samu karin mutum 675 da suka kamu a Najeriya ranar Alhamis

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 675 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –128, FCT-183, Kaduna-85, Kwara-57, Katsina-50, Filato-42, Rivers-39, Kano-33, Ondo-21, Ogun-17, Bauchi-10, Sokoto-5, Edo-2, Ekiti-1, Bayelsa-1 da Delta-1.

Yanzu mutum 71,344 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 65,474 sun warke, 1,190 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 4,680 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 24,366, FCT –7,899, Oyo – 3,747, Edo –2,726, Delta –1,828, Rivers 3,114, Kano –1,874, Ogun –2,292, Kaduna –3,586, Katsina -1,119, Ondo –1,749, Borno –758, Gombe –1,047, Bauchi –802, Ebonyi –1,055, Filato – 3,979, Enugu –1,355, Abia – 926, Imo –681, Jigawa –340, Kwara –1,146, Bayelsa –466, Nasarawa – 539, Osun –962, Sokoto – 189, Niger – 298, Akwa Ibom – 362, Benue – 501, Adamawa – 287, Anambra – 290, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 108, Ekiti –389, Taraba- 195, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.

Tsohuwar ministar Kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala ta yi wa Najeriya da kasashen Afrika albishir cewa lallai nan da watanni uku masu zuwa suma za su samun ruwan maganin rigakafin Korona.

Ngozi ta fadi haka ne da take ganawa da ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama a Abuja.

Ta ce zuwa yanzu kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO, CEPI, GAVI da sauran kungiyoyin bada tallafi na tattauna yadda kasashen da basu da karfi da kasashe masu tasowa kamar Najeriya za su iya samun maganin rigakafin cutar korona da aka hada cikin gaggawa kuma a farashi mai sauki.

A yanzu dai kamfanin Pfizer da AstraZeneca ne Suka hada maganin rigakafin cutar wanda ke da ingancin kawar da cutar.

Ngozi ta ce ana tattauna yadda za a gaggauta samarwa kasashen da basu da karfi da kasashe maso tasowa samu wannan magani kafin karshen farkon wata hudu na shekara mai zuwa.

Share.

game da Author