Gwamnati ta umarci a sake bude wuraren killace masu korona, saboda ta sake darkakowa gadan-gadan

0

Gwamnatin Najeriya ta ce a gaggauta sake bude cibiyoyin killace masu cutar korona, ganin yadda cutar ta sake darkakar kasar gadan-gadan ba sauki.

Ministan Harkokin Lafiya Osagie Ehanire ne ya bayyana haka a wurin taron Kwamitin Dakile Cutar Korona a ranar Alhamis, a Abuja.

Ya ce yin hakan ya zama wajibi, ganin yadda korona ta sake darkakar kasashen Turai gadan-gadan, tamkar wutar-daji.

Ya ce a wannan karo kowa na da rawar da zai taka wajen ganin wannan cuta ba ta sake fantsama ta yi wa al’ummar kasar nan mummunan illa ba.

“Mun ga yadda a ‘yan kwanakin nan ake ta samun karuwar masu kamuwa da cutar korona a kullum a kasar nan. Wannan kuwa ya sa mu tunanin sake barkewar cutar a karo na biyu.

“Dalili kenan na bada umarnin a gaggauta sake bude cibiyoyin killace masu cutar korona da cibiyoyin bayar da magunguna wadanda a baya aka rufe, saboda karancin masu dauke da cutar. Kuma a sake gaggauta kai jami’an lafiya a dukkan cibiyoyin.

Kasahen Turai na ci gaba da samun adadin masu kamuwa da cutar a kullum, fiye ma da yadda aka rika samu a baya.

Kasashe irin su Ingila, Portugal da Hungary tuni sun rigaya har sun kakaba dokar zaman gida tilas, ganin yadda adadin masu kamuwa a kullum har ma ya zarce yawan irin yadda ta rika kama mutane a watannin baya.

Abin ya kara muni da kamari a Amurka, inda a yanzu adadin wadanda su ka kamu a kasar ya haura mutum milyan 15.

Minista Ehanire ya shawarci ‘yan Najeriya su dauki kwararan matakan kare kai, musamman a lokacin Kirsimeti da sabuwar shekara, domin cutar korona ba hutu ta ke dauka ko jin fashin ranar da ba a iya kamuwa da ita ba.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya sha alwashin cewa na Najeriya na sane da irin yadda cutar ta sake barkewar sosai a Turai, kuma ana cikin shiri a kasar nan.

Ya ce duk wasu rigakafi ko maganin korona da za a sayar wa Najeriya, zai kasance sai Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ingancin su tukunna.

“Kuma ko an kawo su a nan kasar, sai likitocin mu da masu binciken magunguna sun auna sun tantance sahihanci tukunna.” Inji Mustapha.

Share.

game da Author