Babban kotu a jihar Kano ta wanke tsohon ministan harkokin Waje, kuma jigo a jam’iyyar PDP, daga zargin handame naira miliyan 950 kudin Kamfen.
Alkalin kotun mai shari’a Lewis Allagoa ya ce EFCC bata bayyana hujjoji masu gamsarwa ba, a dalilin haka kotu bata kama Wali da laicin komai ba.
Tsohon ministan harkokin Waje, Aminu Wali ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fatattaki Boko Haram har sai da ya kai ga ba su iya kai hare-hare a kasar nan.
Wali ya ce tun bayan da Buhari ya zama shugaban kasa matsalar tsaro ya tabarbare a kasar nan.
” Ko maganan sace ƴan matan makarantar Chibok da aka yi idan aka yi zurfin nazari a kai da kyau za a ga ba matsalar gwamnatin tarayya bane. Abu ne da ya auku a jihar Barno, kuma duka yan jihar ne sannan sun san abinda ke faruwa a lokacin.
” Idan dai maganan Boko Haram za ayi, gaskiyar magana itace gwamnatin Jonathan, wato gwamnatin mu a lokacin mun tarkata su basu Iyayin komai ba , babu abinda suke iya yi, dun fada cikin dimuwa da tsoro, duk sun gudu.
” Idan ba a manta ba, a lokacin da aka dage zaben shugaban kasa da makonni biyu, mun yi nasara sosai wajen kawo karshen Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabas, kowa ya shaida haka.
” A dalilin haka idan za a tuna babu wata mazaba da ba a yi zabe ba a 2015 a yankin kaf. Sai bayan mun tafi ne sannan abubuwa suka fara tabarbarewa komai ya lalace kuma da wannan gwamnati ta hau.
Wali ya kara da cewa basu bar gwamnati ba sai da suka tabbatar an ci karfin Boko Haram ba su iya komai.
Bayan haka ya bayyana cewa da gangar ƴan adawa suka yi kutunkutun din ganin ƙasashe kamar su Amurka basu saida wa Najeriya da makamai ba. Sun riƙa kai musu bayan karya domin lalata mu a idanun su kuma hakan yayi tasiri.
” Mun matsa kasar Amurka su saida mana jirgin yaki amma suka ki kememe. Daga nan sai muka garzaya ƙasar Turkiyya. Sun amince su saida mana sai dai an samu matsala a lokaci. Turkiyya ta ce ba za ta iya saida mana ba saboda dukkan su suna sa injina kirar kamfanonin Amurka wanda idan har za su saida mana sai Amurka ta amince tukunna.
Discussion about this post