Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 501 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –218, FCT-112, Kaduna-53, Filato-24, Katsina-21, Kano-16, Yobe-14, Ondo-10, Ogun-9, Edo-7, Bayelsa-5, Ribas-4, Borno-4, Osun-2 da Ekiti-2.
Yanzu mutum 78,434 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 68,303 sun warke, 1,221 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 8,910 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Asabar, Mutum 903 suka kamu a Najeriya, jihohin Kaduna, Legas da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi zaftaran mutane.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 26,708, FCT –9,627, Oyo – 3,788, Edo –2,768, Delta –1,843, Rivers 3,279, Kano –2,032, Ogun–2,382, Kaduna –4,504, Katsina -1,405, Ondo –1,793, Borno –778, Gombe –1,164, Bauchi –897, Ebonyi –1,091, Filato – 4,262, Enugu –1,376, Abia – 980, Imo –734, Jigawa –386, Kwara –1,296, Bayelsa –497, Nasarawa –600, Osun –979, Sokoto – 228, Niger – 381, Akwa Ibom – 395, Benue – 515, Adamawa – 355, Anambra – 299, Kebbi – 143, Zamfara – 79, Yobe – 164, Ekiti –405, Taraba- 203, Kogi – 5, da Cross Rivers – 93.
Akalla mutum 3,656 ne cutar korona ta kashe a ranar Laraba, 16.9 Ga Disamba a Amurka, yayin da mutum 247,403 su ka kamu da cutar duk a ranar ta Laraba.