HIMMA DAI MATA MANOMA: Rashin tsaro ne babban kaubalen mu –Inji wata mai himma

0

A ci gaba da zakulo matan da su ka maida himma wajen kokarin noma, PREMIUM TIMES HAUSA ta zo maku da bayanin wata mai himma wajen noma, mai suna Mercy Nnanna.

Nnanna mai shekaru 35 da yara uku, ta na noman ta ne a karkarar yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Nnanna ba karamar jaruma ba ce idan ta shiga cikin ganar ta. Ta na noma masara, doya da sauran kayan gona daban-daban.

Wannan mata dai ta ce bana shekara bakwai kenan da ta fara noma amfanin gonar ta ke sayarwa. Amma kuma ta ce ita dama tun tashin ta, a cikin noma ta tashi, kasancewa iyayen ta manoma ne.

“Ba ni da gona ta kai na. Amma ina aron gona, kuma miji na ya na da gonaki. Saboda haka wadanda ba zai noma ba, sai ya ba ni na noma. A Kuje na ke noma, amma shekarar da ta gabata har Kwali na je na karbi aron gona na noma.

“A shekarar da ta gabata dai na noma hekta biyar. Wannan shekarar ban samu aron gona ba, don haka sai na yi maleji da hekta uku zuwa hekta uku da rabi kawai.

Nnanna ta ce samun irin shuka ba ya yi mata wahala. “Ina samun irin da n aka shukawa daga Cibiyar Dabarun Noma ta IITA da kuma Hukumar ADP.”

“Idan na noma masara, ina amfani da kusan rabin ta ina ciyar da kaji, saboda ina kiwon kaji. Ina ba su dusar, Koma ka san Arewa ana bukatar masara, su na sarrafa ta su yi abinci kala-kala. Shi ya sa ake da bukatar ta a Arewa.

“Ina kuma noma wake da dawa. Ka san wake ya na da sinadarin gina jiki da karin lafiya. Shi ya sa wanda ya noma wake ba zai yi asara ba.

“Ka san irin noman mu sai a hankali. Ba ni da kayan noma na zamani. Ina yin amfani da tarakta a noma. Ita kuwa wannan tarakta, ta aro ce. Idan a aro tarakta, za a hada ka da direba. Shi wannan direba, idan ka na so aikin sa ya yi kyau sosai, to sai ka kyautata masa. Sannan kuma zan biya kudin hayar tarakta ga kamfanin da na ke aro ta.

“Ni idan ka ga na yi amfani da leburori, to wurin casa ne ko kuma wurin watsa takin zamani. A nan ina kirawo masu aiki, har da yara su yi min aiki na biya su.”

Da ta ke maganar albarkar noma, Nnanna ta ce shekarar da ta gabata dai ta samu amfanin gona mai yawan gaske. Amma wannan shekarar dai abin ba a cewa komai. “Saboda shanu suka cinye min masara, sai buhu 15 kadai na samu.”

“Matsalar wurin ajiya ma ta na damun mu. Amma akwai wani buhu mai nunki uku, wanda yanzu da shi muke adana kayan goma. Ko da yake ba duka kayan abincin da na noma na ke sayarwa ba. Na kan dan ware wanda za mu ci a gida.’’

Ta ce a kasuwar Kuje da Gwagwalada ta ke sayar da amfanin gonar ta. Wani lokaci ta kan bayar ne sai an sayar a biya ta kudin.

“Miji na ya na taimaka min da kudi, kuma ya na karfafa min guiwa. Amma fa babu ruwan sa da raka ni gona. Kai, shi bai ma san inda wasu gonakin nawa su ke ba.

“Gwamnati na taimaka mana da irin shuka, amma sayar mana ta ke yi ta na rage mana kashi 50 bisa 100 na kudin. Wannan shekara an rage mana har kashi 75. Amma abin ba wani abin yin tinkaho ba ne.

Ta ce ba a nuna mata bambanci, amma dai akwai alfanun da namiji kan samu wanda mace ba ta cika samu ba.

“Matsalar da ta fi damu na, ita ce rashin mutuncin makiyaya. Saboda sun taba duka na, kuma su ka sa shanu su ka cinye min amfanin gona. Na san mata da yawa wadanda makiyaya su ka kashe mazan su a gonaki.

“Wannan matsala ta rashin tsaro ita ce babban kalubalen mu. Idan kasa babu tsaro ai noman ma ba zai yiwu har a ciyar da kasar abinci wadatacce ba.” Inji Nnanna.

A matsayin ta na wadda ba hamshakiyar mai nom aba, ta ce abin da ta fi bukata a yanzu shi ne a samar da tsaro, sai kuma tallafin harkar noma da kuma lamunin kudi domin bunkasa harkokin ta na noma.

Share.

game da Author