Duk da yadda matsalar garkuwa da mutane ta zama ruwan-dare a sassan kasar nan, Mai Taimakawa Na Musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari a Fannin Yada labarai, Garba Shehu, ya bayyana cewa Buhari ya nuna jarunta wajen iya samar a tsaro da tsare Najeriya.
Cikin wata sanarwa da ya tura wa PREMIUM TIMES a ranar Lahadi, Shehu ya lissafa wasu batutuwa biyar dangane da yadda aka ceto daliban Kankara su 344 cikin gaggawa da ya ce hakan nuna jarunta da karfin iyawa ce da Shugaba Buhari ya nuna.
Shehu ya ce nasarar ceto yara 344 da aka yi, abin murna da tinkaho a kowace kasa ce a duniya, inda siyasa ba ta rufe idon wasu ‘yan-ba-ni-na-iya ba.
Ya ce Najeriya ta yi murna, ganin yadda Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya aiko da sakon taya murnar ceto daliban.
Abu na farko, Shehu ya ce ceto wadannan yara ya nuna Buhari na da jarumtar iya tsare Najeriya, duk kuwa irin halin da kasar ke ciki.
Abu na biyu, Shehu yace tilas a yaba wa sojojin Najeriya, duba da irin gagarimar rawar da su ka taka wajen ceto yaran. Ya ce kamata ya yi a rika yi masu jinjina, domin a ganin sa, ba a yaba masu kamar yadda ya kamata.
Abu na uku shi ne ceto yaran ya nuna ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda duk ta su ta kusa karewa, domin a yanzu dai ba su da wurin gudu. Kuma ko sun gudu, ba su da wurin boyewa, domin sojojin mu za su iya cim masu.
Shehu ya kara da cewa abu na gaba shi ne irin so da kaunar da ake wa Shugaba Buhari a kasar nan, na nan daram, bai ragu ba. Kuma ana yi masa kallon shi ne dai jagoran da zai kai kasar gaci, ya tserad da ita zuwa tudun-mun-tsira.
Abu na biyar kuma Shehu ya ce akwai wasu mutane ‘yan kalilan masu fatan wani sharri ya samu kasar nan, domin kawai su samu abin fadi da sunan adawa. Ya ce wannan ceto yara da aka yi, ya kunyata irin wadannan mutane.