Idan Har Buhari Bai Farka Ba, Sai Ya Nemi Masoyi Daya Ya Rasa A Cikin Talakawan Najeriya, Daga Bashir Dambam

0

….Matsalar Rashin Tsaro Da Tsadar Rayuwa Sune Suka Janyowa Buhari Bakin Jini Da Jam’iyyar APC Gaba Daya A Wajen Talakawan Najeriya

Magana ta gaskiya itace indai har Buhari bai farka daga baccin da ya ke yi ba, Sannan bai sauya salon mulki ba, kuma bai sauya wasu daga cikin makusantan sa ba (Masu bashi shawara) to ina ji a raina kafin ya sauka akan mulki zai nemi masoyi daya ya rasa cikin Talakawan Najeriya.

Dalilina kuwa shine a yanzu babu wani talaka dake rayuwa acikin najeriya wanda zai fito ya bugi kirji yace lallai yana alfaharin samun buhari a matsayin shugaban kasa, Sannan ya nuna wani abu guda yace wannan ya sameshi ne a adalilin mulkin Buhari.

Banajin akwai wani sauki ta ko wani fanni da talakawan Najeriya suka samu adalilin zaman buhari tsawon shekaru shida (6) a shugaban kasa. Komai cewa sukeyi jiya tafi yau, Bahaushe kuwa yace kowa ya tuna bara tofa beji dadin bana ba.

Anyi shekara da shekaru ana abu daya kullum babban kalubalen da kasar Najeriya take fuskanta shine Matsalar tsaro sama da shekaru 10 amma abu yaki ci yaki cinyewa daga wannan sai wancan, ana tare wadannan sai wasu su bullo.

Nasan dayawa daga cikin mutane suna da sani akan cewa babban abin daya fara janyowa tsohon shugaban kasar Najeriya good luck Jonathan dama jam’iyyar PDP bakin jini a wajen mutanen arewa shine Matsalar tsaro da kashe kashen al’umma da aka fuskanta a lokacin mulkinsu.

Sannan kuma abinda ya karawa Shugaba Muhammadu Buhari farin jini a wajen talakawan arewa shine a wannan lokaci Yan kasa suke cikin barazanar rashin Tsaro suna ganin Shugaba Buhari shine kawai zai kawo musu mafita akan matsalar tsaro da kasa take fuskanta idan har ya samu damar zama Shugaban kasar Najeriya, tare kuma da la’akari da irin furucin daya keyi na cewa shine kadai zai iya.

Wanda kusan adalilin hakan ya janyo ra’ayin maza da mata suka fito sukayi zabe da sa rai akansa, na samun sauki ta ko wace fuska.

Amma ayau an wayi gari matsalar tsaro harma tanaso tafi yadda aka fuskanta a gomnatin data gabata.

Farin jinin da Buhari yake dashi da jam’iyyar APC a wajen talakawa acikin Kashi 100 yanzu befi 40 ba, badon komai ba sai sbd kara tabarbarewar abubuwa da ake samu a ko wace rana.

Domin duka mun sani, Buhari talakawa sun nuna masa irin soyayyar da tunda aka fara Mulkin Dimokaradiyya a Najeriya ba’a taba nuna ma wani dan siyasa irinta ba. A 2015 indai a jam’iyyar APC dan siyasa ya fito neman zabe to ko beyi campaign ba guguwar chanji ta kaishi a dalilin farin jinin BUHARI.

Amma wanda aka nuna masa irin Wannan soyayyar a yau an wayi gari Talakawa suna gudunsa, suna Allah wadai da irin mulkinsa harma wasu suna cewa gara gomnati baya akan tasa., wasu suna kiran gomnatinsa azzalumar gomnati, wasu suna kiransa da mugu, wasu suna kiran gomnatinsa da marar tausayin gomnati, badon komai ba sai sbd irin halin matsi da kunci da Talakawa suka tsinci kansu aciki kuma suke kara fuskanta a ko wace rana.

Shin anya shugaba BUHARI yasan da wannan kirari da akeyiwa gomnatinsa?

Shin ko Shugaba BUHARI yasan talakawa suna cewa gara gomnatin baya da suka guje akan tasa?

Shin anya shugaba BUHARI yasan cewa ya janyowa jam’iyyar sa ta APC bakin jini a wajen Talakawa ?

Shin anya shugaba BUHARI yana da masaniya akan irin Shirin da Talakawa sukeyi na hambarar da duk wani dan takarar daya fito a jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.?

Shin anya shugaba BUHARI yasan halin kunci da matsi da firgici da Talakawan Najeriya suke ciki?

Idan kuwa ya sani to tabbas talakawa suna da hujjar daukan duk wani matakin daya dace wajen nemawa kansu mafita tunda gomnatinsa ta kasa.

Domin kuwa a satin daya gabata naci karo da wani labari cewa wani mutumin dayawa sanyawa dansa suna BUHARI ya sauya masa sunan zuwa wani daban, haka mutane da sukayi ta tura masa kudi duk sunce sunyi nadamar turawa.

Ko meya janyo hakan..?

Ko BUHARI yasan da hakan.

Daga karshe inaso nayi amfani da wannan dama na bawa mai girma Shugaban kasa shawara daya duba Wannan al’amari yayi Kyakkyawan nazari akai, domin wlh idan har ya sauka beyi wani abinda Talakawa zasu amfana dashi ba to fa lallai akwai wadanda har su mutu suna masa Allah ya isa.

Akwai matsaloli na kusa da talakawa da suke damunsi akoda yaushe, su yakamata ya maida hankali akai, ba aikin jiragen kasa ba,

Ina fatan mai girma Shugaban kasa zai duba wannnan Al’amari.

Ya Allah ka kawo mana mafita.

Allah ka ciyar da kasarmu gaba, Amin….

Share.

game da Author