ZABEN NIJAR: Namadi Sambo zai jagoranci tawagar ECOWAS zuwa Nijar

0

Tsohon Mataimakin Shugaba Kasa, Namadi Sambo zai jagoranci tawagar Kungiyar ci gaban Kasashen yankin Afrika ta Yamma zuwa kasara Nijar domin kula da zaben kasar da za a yi nan da makaonni masu zuwa.

Namadi ya ziyarci fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin ya domin sanar da shi wannan aiki da ECOWAS suka bashi.

A jawabin sa, Namadi Sambo ya jinjina wa shugaban kasar Nijar Momoudou, kan dagewa da yayi da bin dokokin kasar sa na sauka daga kujerar mulki bayan ya kammala wa’adin sa na zango ta biyu.

” Ni dan asalin garin Daura ne, muna makwabtaka da kasar Nijar, na san komai game da Nijar, saboda haka muna taya su murna matuka kuma muna rokon Allah ya sa ayi wannan zabuka lafiya.

A karshe tsohon mataimakin shugaban Kasa Namadi Sambo ya mika taya murnar sa ga shugaba Buhari, bisa ceto yaran makarantar kankara da aka yi da kuma murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

Share.

game da Author