Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyar sa ga Iyalai da ‘Yan uwan marigayi Saidu Kumo.
An bayyana sanarwar rasuwar Sanata Saidu Kumo, ranar Lahadi.
Kumo ya rasu ya na da shekara 71 a duniya.
Buhari ya ce ba zai manta gwagwarmayar da Sanata Kumo yayi a zaben 2019 na tabbatar da nasarar APC a zabukan da aka yi ba.
A karshe yayi fatan Allah ya ji kan sa.
Ya rasu a asibitin Gwagwalada, inda ya ke jinyar rashin lafiya.
Kumo yayi sanata tsakanin 1999 zuwa 2003, inda ya wakilci Mazabar Gombe ta Tsakiya, karkashin jam’iyyar APP, wadda daga baya ta koma ANPP.
Ya rike mukamin mashawarci na musamman ga tsohon Shugaban Kasa, Umaru Yar’Adua na wani takaitaccen lokaci, a cikin 2008.
Saidu Kumo yaya ne ga Tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya, Aliyu Modibbo, Danburam Gombe.
Haka nan kuma ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan marigari Madawakin Keffi, Abubakar Senior wanda shima Allah yayi wa rasuwa.
Allah ya gafarta musu, Amin.