Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bayyana yadda aka sace Faston a katafaren filin addu’o’in musamman dake fadan Kagoma.
Aruwan ya ce maharan sun rika harbi ta koina a lokacin da suka dira filin taron.
Shi kuma kakakin ‘yan sandan Kaduna, Muhammed Jalige ya shaida cewa an ceto faston da matarsa da misalin karfe biyun rana, ranar Lahadi.
Ya ce ba a biya ko sisi ba.
Idan ba a manta ba, Mahara sun sace faston cocin ‘Pentecostal Fellowship’ Emmanuel Bako da matar sa Sandra.
Maharan sun tarke fasto Emmanuel da Matarsa Sandra a filin taro da addu’o’in musamman na Kirsimeti mai suna Albarka camp, Fadan Kagoma, kusa da Kafanchan karamar hukumar Jema’a.
Kakakin rundunar’yan sandan Kaduna Mohammed Jalige ya tabbatar da wannan al’amari, sannan ya kara da cewa maharan sun afka wa filin taron ne da wajen karfe 8:30 na dare, ranar Kirsimeti.
Bayan fasto Emmanuel da matarsa Sandara, akwai wani mutum daya da maharan suka arce da shi.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da aukuwar haka.
Ya ce jami’an tsaro ne suka fatattaki maharan sai dai Allah bai basu sa’an cimma musu ba har suka gudu.
Jihar Kaduna ta yi kaurin suna wajen hare-haren ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.