TONON ASIRI: An kama wani Dagaci cikin gungun mahara a lokacin batakashi da ‘Yan sanda

0

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja,Wasiu Abiodun ya bayyana yadda ‘yan sanda suka cafke dagacin garin Tungan Iliya dumu-dumu tare da mahara a wajen batakashe da ‘yan sanda.

” ‘Yan sanda sun tirke gungun mahara a maboyan su cikin dajin Tunga Iliya, a nan ne fa bayan sun bude musu wuta, suma maharan suna maido wuta, har Allah ya ba ‘yan sanda sa’an fin karfin su.

” Bayan ‘yan sanda sun yi wa maharan zobe sai suka kutsa cikin dajin canciki inda suke boye, sai ko kwatsam suka iske harda Dagacin garin cikin maharan da shi ake ta batakashi da ‘Yan sandan.

Abiodun ya ce sun kama mahara 10, uku sun gudu amma fa da rauni a jikin su.

Kuma an kama wata mata mai suna Sumayya Bello da ke kai wa mahara bayanan sirri daga cikin gari.

A karshe Abiodun ya ce za a ci gaba da bincike akai.

Share.

game da Author