An kara wa tsohon Shugaban EFCC mukami zuwa Mataimakin Sufeto Janar din ‘Yan Sanda

0

Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Mohammed Adamu ya amince da karin girman da aka yi wa wasu manyan jami’an yan sanda su biyar, ciki har da tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde, kuma ya tura kowane wurin aikin sa.

Kakakin Hukumar Yan sanda Frank Mba ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, a Abuja.

“Sabbin Mataimakan Sufeto Janar din su biyar da kuma wuraren aikin da aka tura kowanen su, sun hada da – tsohon Shugabanb Hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde, wanda aka tura shugabancin Shugaban Sashen Binciken Sirri, sai Usman Baba, Shugaban Binciken Manyan Laifuka, sai kuma David Folawiyo, Shugaban Sashen Ayyukan Fasahar Zamani (ICT),

“Sauran sun hada da Joseph Egbunike, Shugaban Bangaren Kudaden da Tsare-tsaren Aikin Ofis, sai na biyar Danmalam Mohammed, Shugaban Bangaren Bayar da Horo da Bunkasa Aikin ’Yan Sanda.”

Sufeto Janar ya gode masu, kuma ya taya su murnar wannan karin girma da aka yi masu, tare da fatan zai kara zaburar da su ga gudanar da aiki tukuru,

Lamorde shi ne Shugaban EFCC wanda ya gadi Farida Waziri.

Share.

game da Author