Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a sabuwar dokar zabe. Sabuwar dokar ta kafa ka’idar cewa, “duk mataimakin shugaban kasa ko mataimakin gwamnan da ya gaji kujera, to idan ya shekara hudu, zai hakura, ba zai sake shiga takara zango na biyu ba.
Wannan doka kenan ta na nufin idan har Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osingajo ne ya tsaya takara a 2023 a karkashin APC kuma ya yi nasara, to shekara hudu kadai zai yi, ba zai sake takara zango na biyu ba.
Haka nan kumaidan Mataimakiyar Gwamnan Kaduna, Hadiza Balaraba ce ta fito wa APC takara a jihar Kaduna har ta yi nasara, to ba za ta sake tsayawa takara a zango na biyu bayan ta yi shekara hudu ba.
Wannan doka na daya daga cikin kudirori uku da Buhari ya sanya wa hannu a ranar Juma’a, kuma duk su ka zama doka a Najeriya.
Duka dokokin uku na da nasaba da kudirorin da su ka shafi zabe, kafin zaben da kuma bayan gudanar da zaben.
Babban Mai Taimakawa Ga Buhari kan Harkokin Majalisar Dattawa Ita Enang ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, inda ya ce dokar farko ta shafi batutuwan harkokin zabe ne, amma na share-fagen zabe, kafin yi zaben kenan.
“Wata doka da ta fara aiki a yau ita ce kwaskwarima ta 21 da aka yi wa Kundin Tsarin Mulki. Dokar ta rage zawon kwanaki da watannin da za a shafe ana rigingimu, markabu da shari’u. Sabuwar dokar za ta tabbatar da cewa an gama komai har shari’un tun kafin ranar zabe.”
“Sannan kuma kudiri na 16 wanda Shugaba Buhari ya sa wa hannu ya zama doka a yau, shi kuma zai tabbatar da cewa ko mataimsakin shugaban kasa da ya gaji shugaban sa a mulki, ko mataimakin gwamnan da ya gaji mulki bayan kammala wa’adin gwamnan, to zango daya na shekarun hudu zai yi, bai zai sake neman takara karo na biyu ya zarce ba.
Wannan doka kenan ta haramta wa Shugaba Goodluck Jonathan sake tsayawa takara. Saboda ya yi mataimakin Shugaba Umaru Yar’adua, ya hau mulki bayan rasuwar Umaru, kuma ya yi zango daya bayan ya ci zabe daga 2011 zuwa 2015. Amma kuma ya fito takara a 2015, amma Buhari ya kayar da shi.
Sabuwar dokar ta ce INEC ta na da kwanaki 21 ta gudanar da zaben cike gurbi maimakon kwanaki bakwai.
Discussion about this post