Sake barkewar cutar korona gadan-gadan a kasar nan ta haifar da sanarwa cewa kada daliban jami’a su yi gaggawar komawa makarantu. Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ce ta fitar da wannan sanarwa.
NUC ta ce duk da a yanzu an cimma matsayar sasantawa tsakanin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa da kuma Gwamnatin Tarayya, to dalibai su ci gaba da zama a gida, babu batun gaggawar sake bude jami’o’i bayan Kirsimeti da bukukuwan sabuwar shekara.
Wannan sanarwa da NUC ta fitar, ta zo ne ganin yadda korona ta sake barkewa fiye da yadda ta fantsama a farkon bullar ta.
Cikin makon da ya gabata dai an samu wadanda su ka kamu da cutar korona fiye da mutum 5000 a Najeriya, adadin da ba ta taba samun yawan haka a cikin mako daya a kasar nan ba.
NUC ta kuma umarci Shugabannin Jami’o’i kada su bari ana gudanar da wasu tarurruka a cikin jami’o’in wadanda dandazon jama’a za su yi cincirindo a wurin.
Sanarwar da Mataimakin Shugaban NUC a fannin Tsarin Mulki, Chris Maiyaki ya sa wa hannu, ya umarci shugabannin jami’o’i cewa dukkan dakunan kwanan dalibai, ajujuwan karatu da dakunan taro su ci gaba da kasancewa a kulle.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda cikin makon da ya gabata, korona ta kashe likitoci 20 a Najeriya.
Yayin da cutar korona ta dawo gadan-gadan, Shugaban Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA), ya bayyana cewa likitoci 20 su ka mutu a wannan makon sanadiyyar cututtuka masu alaka da korona.
Enema Amodu ya bayyana wannan tashin hankali a ranar Juma’a wurin taron manema labarai, inda ya ce wadanda su ka mutu din sun hada da jami’an lafiya da na tuntuba da wasu farfesoshi da tantagaryar likitoci.
Ya ce yawan wadanda ke mutuwar na karuwa a kullum.
“Mu da ke aikin harkokin kula da lafiya, mun rasa abokan aikin mu da dama. Wadanda korona ta kashe a cikin mako daya kadai a fadin kasar nan, sun kai likitoci 20.” Inji shi.
Jami’an kiwon llafiya na fadawa tarkon saurin kamuwa da cutar, saboda su ne ke fara tunkarar wanda ya kamu da cutar.
Duk da cewa su kan su jami’an kula da lafiya da likitocin su kan su ana gargadin su rika amfani da rigunan kariya daga hada jiki da wanda ya kamu da korona, da yawan su ba su da sukunin samun kayan kariyar.
Idan ba a manta ba, sama da jami’an kula da lafiya 1,000 ne su ka kamu da cutar korona a Najeriya.
Hukumar Kula da Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (WHO), ta ce zuwa Yulin da ya gabata sama da jami’an kula da lafiya 10,000 ne suka kamu da cutar korona a fadin Afrika.
Sai dai zuwa yanzu ba za a ma iya tantance adadin yawan jami;an kiwon lafiyar da su ka kamu ba a Najeriya.
Amodu yay i gargadin a tashi tsaye wajen kare kai daga kamuwa, domin a yanzu da korona ta sake dawowa, ta fi ta baya karfi da saurin kassara mutane gadan-gadan.
Ya ce a yanzu jama’a ba su daukar matakan kariya da muhimmanci, kuma babu kayan kariyar a wurare da dama, kamr yadda aka rika sayarwa a watannin baya, farkon bullar cutar.