TSANANIN RASHIN TSARO: Gwamnoni, Shugaban Majalisar Dattawa da Sarakunan Arewa sun yi taro a Kaduna

0

Gwamnonin Arewa da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da kuma wasu sarakunan Arewa masu daraja ta daya, sun yi taron neman mafita a Kaduna.

Taron wanda aka yi a Zauren Taro na Sa Kashim Ibrahim, ya samu halartar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari.

Sauran jiga-jigan da su ka halarci taron akwai Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Mohammed Bello, Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, sai Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Muhammad Adamu.

A bangaren Sarakunan Gargajiya, akwai Sarakunan Gwandu, Zazzau, Hadeja, Bauchi da Etsu Nupe daga Jihar Neja.

PREMIUM TIMES ta ji cewa taron zai magana ne kan batun tsaro da kuma lalata kayan da aka yi a wasu garuruwan Arewa, sakamakon barkewar zanga-zangar #EndSARS.

Gwamna mai masaukin baki, Nasir El-Rufai, ya ce taron zai maida hankali kan barnar da masu zanga-zanga su ka yi a garuruwan Arewa da kuma batun maganar tsaro.

El-Rufai ya ce za a tabo batun inganta rayuwa da tattalin arzikin yankin.

A shafin Twitter na Masarautar Hadeja, an bayyana cewa matsalar tsaro na kara haifar da sakwarkwacewar tattalin arziki da inganta rayuwa a Arewa.

“Jihohin Arewa da dama na fuskantar matsalar tsaro. Ayyukan ta’addancin mahara da garkuwa da mutane na haifar da gagarimar barazana ga yankunan karkara da kuma birane da garuruwa.

“Yan bindiga na ta matsa kaimi wajen ragargaza tattalin arzikin rayuwar mutanen karkara ga mamoma a gonaki da gidajen su.”

Share.

game da Author