Za a rika baiwa masu Kanjamau maganin da zai dauke su tsawon watanni uku – Inji Kungiya

0

Kungiyar masu fama da cutar Kanjamau na Najeriya ta bayyana cewa daga yanzu asibitoci za su rika baiwa masu dauke da cutar maganin da za su rika sha na tsawon watanni uku nan take.

Shugaban kungiyar Kenna Nwakanma ya Sanar da haka yana mai cewa wannan tsari da aka fara yanzu zai taimaka wajen rage cinkoso da yawan aiki da jami’an lafiya ke fama da su a asibitoci.

Nwakanma ya ce wannan sabon tsarin zai taimaka wajen rage matsalolin karancin magani da rashin samun kula da masu dauke da cutar ke fama da su a kasar nan.

Ya mika godiyarsa ga gwamnati bisa wannan tsari da ta samar musamman yadda kungiyar ta dade tana kai kukan ta wajen gwamnati domin inganta kulan da masu fama da cutar ke fama da su a kasar nan.

Bayan haka Nwakanma ya ce wasu asibitocin ba su fara bada maganin cutar kamar yadda sabon tsarin yake.

Sannan har yanzu wasu jami’an lafiya na karban kudin magani a hannun masu fama da cutar kafin a basu magani maimakon kyauta.

Ya yi kira ga duk asibitocin da basu fara amfani da sabon tsarin bada maganin ba da su yi gaggawar yin haka a kasar nan.

A watan Maris din shekarar 2019 PREMIUM TIMES ta wallafa cewa akwai akalla mutum miliyan 1.9 ne ke dauke da kanjamau a kasar nan.

Hukimar hana yaduwar cutar ta kasa (NACA) ce ta fitar da wannan alkaluma a watan Maris 2019.

Share.

game da Author