Soja ya jibgi wata mace dalilin yin shiga ta fitsara

0

Wani sojan Najeriya ya takarkare ya rika zabga wa wata mata zabgegiyar bulala, a filin da aka tura shi tabbatar da bin doka da oda a zanga-zangar #EndSARS.

Lamarin ya faru ne a jihar Oyo, inda jama’a su ka dauki bidiyon yadda ya ke lakada wa matar dukan tsiya, bisa dalilin yin shiga ta fitsara.

Ya lakada mata dukan tsiya ne a Beere, Ibadan inda majiya ganau ta shaida wa PREMIUM TIMES.

An ga wani soja na lakada wa wata mace dukan dukan tsiya, yayin da wasu sojojin na ta hakilon aske zankon sumar da ke kan su da almakashi.

Bidiyon ya nuno wani soja ya tilasta wata mace zama a kasa, shi kuma ya na zabga mata bulala a duwaiwan ta. Bulalar dai an fi bada karfin fahimtar cewa bel ce ya ke zabga mata.

Share.

game da Author