TITIN ABUJA-KANO: Katsalandan din da Sanatoci suka yi mana ya sa aikin ke tafiyar hawainiya – Fashola

0

Ministan Ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ya bayyana cewa dalilin da ya sa aikin sake gina titin Kano-Kaduna-Abuja yake tafiyar hawainiya shine sake tsarin hanyar da aka yi bayan na farko.

Fashola ya ce da ace an bi yadda aka tsara aikin tun farko ne da yanzu a ana gaba da kammala shi.

” An riga an gama komai sannan su kansu ƴan kwangilan sun dira kan hanyar zasu fara aiki sai sanatoci suka a maida aikin kowani bangare akalla motoci hudu zasu iya wucewa. Suka mika kukan su ga shugaba Buhari, daga nan sai ya amince a kara fadin titin.

” A dalilin haka ya sa dile sai da aka sake zanen hanyar daga farko har karshe ta yadda za a saka sabbin gadoji 40 a dalilin fadada titin da za ayi.

Fashola ya ce sake yin wannan zane da zai hada da karin da aka yi shi kan sa dole sai an bi doka wajen dauko kamfanin da zai yi aikin. Hakan kawai shima aiki sai an yi ta jire-jire kamar yadda doka ta tsara.

” Tafiya kawai tsawon kilomita 375 ne haka dawowa. Idan ka tara shi sau hudu, yana nufin za a gina titi ne mai tsawon kilomita 1500 daga Abuja zuwa Kano.

Titin Bypass dake Kaduna

An yi wa Fashola tambayar ko me yasa ba a gina titin Bypass dake Kaduna ba sai ya ce: ” Wannan titi dai ko da aka bijiro da yin aikin sa, gwamnan Jihar Nasir El-Rufai ya yi wuf ya ce zai yi gyaran titinin. Bayan duk mun saduda sai ya dawo ya ce mana kuma wai bai samu kudaden da ya ke zaton zai yi amfani da su wajen aikin ba. Dole aka sake sabon lale, sai aka saka hanyar a wani tsari na bashin kudin haraji ne zai yi hanyar.

Ana ta jawabin Ministar Kudin Kasa , Zainab Ahmed ta bayyana cewa ma’aikatar za ta tabbatar an samar wa wannan aiki kudi domin a samu a kammala shi kamar yadda aka faro shi.

Da Fashola da Zainab duk sun yi hasashen lallai za a kammala aikin nan da kafin Buhari ya kammala wa’adin mulkin sa a 2023.

Share.

game da Author