Tabbatattun bayanan bin diddigin yadda ake karkatar da kudaden gwamnati sun nuna Hukumar Kula da Yankunan Kan Iyakokin Najeriya (BCDA), ta yi wa ma’aikata watandar naira milyan 39 ta haramtacciyar hanyar da dokar Najeriya ta haramta.
BCDA dai ta na karkashin shugabancin Junaid Abdullahi, wanda surukin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne, wanda kuma aka nada a ranar 22 Ga Satumba, 2018.
Ita dai hukumar ta ce kudaden alawus din ayyukan duba-gari ne, wato DTA. Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa wannan ikirari da BCDA ta yi ba gaskiya ba ne.
A ka’idar aikin gwamnatin tarayya, alawus din DTA ana yanka shi ne daidai matakin albashin ma’aikaci, kuma mafi yawa shi ne N35,000.
Wannan Naira 35,000 fa shi ne alawus din Ministoci, Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya da sauran manyan jami’an gwamnati masu matakin albashi daidai da su.
Kenan idan ma aka ce wani jami’in hukumar na kan hanyar karakainar duba-gari har tsawon kwanaki 92 daga Oktoba, Nuwamba har zuwa Disamba, to alawus din sa ba zai wuce naira milyan 3.2 ba, a lissafin naira 35,000 kowace rana.
To amma jami’an da aka yi wa watandar kudaden sun samu fiye da wannan adadi, kuma babu inda aka nuno wanin su ko dukkan su sun fita aikin duba-gari tsawon kwanaki 92 a jere.
Misali, an dumbuza wa Murtala Ahmed Baba naira milyan 20.1 a cikin watanni hudu.
Shi kuma daraktan tsare-tsare na hukumar, Ibrahim Kwajafa, an gabza masa naira milyan 12.1.
Shugaban bangaren watsa labarai, Israel Bob-Manuel, an tura masa naira milyan 3.8. Kuma haka aka tura wa Shugaban bangaren gudanarwa, Saubanu Sulaiman Lawal.
Hakan ya kauce wa Dokar Aikin Gwamnati ta 7 da ke Sashe na 723 na Dokar Aikin Gwamnatin Tarayya mai batun karya ka’idojin tasarifin harkokin kudade.
Kenan wannan doka ta hana hukuma ko ma’aikata tura wa jami’an ta kudade kai tsaye a cikin asusun ajiyar su.
Hukumar BCDA dai an kafa ta domin bunkasawa da sa-ido kan yankunan garuruwan da ke kan iyakokin kasar nan.
Sai dai an sha samun hukumar dumu-dumu cikin harkallar makudan kudade a baya.
Cikin shekarar PREMIUM TIMES ta buga yadda aka rika gabza kwangiloli ga kamfanonin bogi da wadanda ba su cancanta ba. Kuma shi kan sa Abdullahi, surukin Buhari din da aka ritsa shi, ya amince an yi ba daidai ba a wajen bayar da kwangilolin da kuma kauce hanya wajen fitar da kudaden wajen fitar da kudaden.
A lokacin BCDA ta bada kwangilar naira bilyan 1.3 ga kamfanoni 33 da kwata-kwata ba su cancanta ba, ko takardun
shaidar biyan haraji ba su da ita.
Discussion about this post