Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 169 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –17, FCT-42, Kaduna-74, Kano-8, Ogun-6, Oyo-6, Rivers-6, Ekiti-3, Bauchi-3, Katsina-2, Delta-1 da Ondo-1
Yanzu mutum 66974 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 62,585 sun warke, 1,169 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,220 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 23,083, FCT –6,671, Oyo – 3,721, Edo –2,696, Delta –1,824, Rivers 2,969, Kano –1,789, Ogun –2,202, Kaduna –3,019, Katsina -1,012, Ondo –1,728, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi – 765, Ebonyi –1,055, Filato -3,813, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –662, Jigawa – 331, Kwara –1,096, Bayelsa – 445, Nasarawa – 488, Osun –945, Sokoto – 165, Niger – 296, Akwa Ibom – 339, Benue – 496, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 94, Ekiti – 357, Taraba- 157, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.
A cigaba da kokarin yadda za a dakile yaduwar Korona a Najeriya da kuma sanar wa mutane bayanan gaskiya game da annobar gwamnati tare da hadin guiwar UNICEF sun samar da wata layin kira na waya da za a rika samun labarin gaskiya game da cutar.
Mutum zai aika da sakon ‘Coronavirus’ zuwa lambar 24453, daga nan za a aiko masa da sakonni game da cutar da matsayin da duniya ke ciki da kasa Najeriya.
Domin shiga wannan dandali a facebook ko Kuma WhatsApp za a iya aikawa da sakon ‘Coronavirus’ zuwa ga +234 908 740 1607. Ko Kuma ta adireshin U-Report kamar haka @ureportnigeria
Wakilin asusun UNICEF a Najeriya Peter Hawkins ya gargadi mutane da su cigaba da kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar korona cewa yin haka ne kadai mutum zai iya samun kariya daga cutar.