Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ce bayan jam’iyyu sun kammala zaben ‘yan takaran su, za kuma abi kowannen su ayi masa gwajin ko yana maskewa wato shaye-shaye.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammed Garba ya bayyana haka bayan ganawar kwamitin Zartaswar jihar.
Garba ya ce gwamna Ganduje ya bada wannan umarni ne domin a kauda matsalar shaye-shaye da ake fama dashi a jihar.
” Za a yi wa kowani dan takara gwajin ko yana shaye-shaye. Idan kuma aka samu a jinin sa akwai alamun haka, za a dakatar dashi daga takara sannan akai shi inda za a kula da shi har ya warke tas-tas.
Bayan haka gwamnati ta amince a fidda kudi don kammala ginin hukumar kula da makarantun Islamiyya ta jihar.