Elisha Abbo, Sanatan da ya gaura wa mace mari a wani kanti ya koma APC

0

Sanata Elisha Abbo daga jihar Adamawa, wanda aka zaba a karkashin PDP, ya koma APC.

Abbo ya bayyana haka a cikin wata sanarwar wasika wadda ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, kuma shugaban ya karanta a farkon fara zaman zauren Majalisar Dattawa a yau Laraba.

Cikin wasikar wadda ana karantawa Sanatocin APC na shewa da arereyya, Elisha Abbo ya ce ya fice daga PDP saboda bahagon jagoranci da Gwamna Ahmed Fintiri na Adamawa ke wa jam’iyyar da jihar, abin da ya ce shi ya janyo rikicin siyasa a jam’iyyar a jihar Adamawa.

Ya kara da cewa ya fahimci babu wani shugaba da ya kula da al’ummar Najeriya kamar Shugaba Muhammadu Buhari.

Abbo ya bada misali da tallafin Tradermoni da sauran tallafin da gwamnatin Buhari ke bayarwa, wadanda ya ce gwamnatocin baya ba su taba yin kwatankwacin haka ba.

“Saboda haka daga yau Laraba, 25 Ga Nuwamba, 2020, na fice daga jam’iyyar APC, na koma jam’iyyar PDP.

Idan ba a manta ba, cikin 2019 ne rikici ya barke cikin wani kantin sayar da maganin karfin maza, lokacin da Sanata Elisha Abbo ya raka wasu mata domin su sayi azzakarin roba, wadda aka kira tabarya-dakan-maza.

An samu sabani har Sanata Abbo ya gaura wa wata mata mari, daga cikin masu tsaron kantin, abin da har ya kai su kotu.

Share.

game da Author