KORONA: Makarantu masu zaman kansu sun rage Kashi 25 na jimlar kudin makaranta ga kowane dalibi a jihar Kano

0

Kungiyar masu makarantun dake zaman kansu a jihar Kano APSON ta bayyana cewa za ta rage Kashi 25 na kudin makarantar da kowani dalibi yake biya a makarantun na jihar.

Kungiyar ta amince da haka ne bayan gwamnati ta yi barazanar soke rukunin karshe na karatun dalibai Idan makarantun ba su rage kudin makaranta ba.

Kakakin ma’aikatar ilimi Aliyu Yusuf ya ce kungiyar APSON ta yi wa iyaye wannan albishir ne a lokacin da shugabannin kungiyar suka kaiwa kwamishinan ilimin jihar ziyara a ofishinsa a Kano.

Mataimakiyar shugaban kungiyar Maryam Magaji ta ce rage kudin makaranta da gwamnati ta umurce su yi zai taimaka matuka wajen ba iyaye daman biyan kudin makarantan yaran su.

Da yake jawabin sa, kwamishinan ilimi Sanusi Kiru ya godewa kungiyar da nuna goyon baya da ta ba gwamnati wajen tausaya wa iyaye da suka yi.

Sai dai dama ya ce idan da ba su rage kudin makarantan ba na wannan rukuni, akwai yiwuwar gwamnati ta soke rukunin karshe, kowa ya dawo shekara mai zuwa.

Jihar Kano na daga cikin jihohin da suka fara sanar da bude makarantu a jihohin su tun bayan kulle su da aka yi a dalilin barkewar annobar Korona a duniya.

Yanzu kusan duka jihohin kasar nan sun bude makarantu domin yara su koma karatu.

Share.

game da Author