Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 72 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –51, FCT-6, Ogun-4, Kaduna-3, Niger-2, Ondo-2, Filato-2, Katsina-1 da Oyo-1
Yanzu mutum 63,036 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 59,328 sun warke, 1,147 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 2,561 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 21,338, FCT –6,124, Oyo – 3,452, Edo –2,666, Delta –1,814, Rivers 2,831, Kano –1,747, Ogun –2,051, Kaduna –2,658, Katsina -953, Ondo –1,669, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 713, Ebonyi –1,049, Filato -3,652, Enugu – 1,314, Abia – 898, Imo –616, Jigawa – 325, Kwara – 1,069, Bayelsa – 413, Nasarawa – 482, Osun –929, Sokoto – 165, Niger – 276, Akwa Ibom – 295, Benue – 493, Adamawa – 252, Anambra – 277, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 335.
Taraba- 146, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
A wannan lokaci da gwamnati ke samun nasara wajen rage yaduwar cutar korona a kasar nan ta yi kira ga mutanen da kada su karaya wajen kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar.
Gwamnati ta ce ci gaba da kiyaye sharaddun guje wa kamuwa da cutar ce kadai hanyar da wannan ƙasa za ta samu nasaran rabuwa da cutar.
Hanyoyi 10 don gujewa kamuwa da cutar.
1. Yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu.
2. Rufe hanci da baki idan za ayi atishawa.
3. A wanke kuma a dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.
4. Rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya.
5. A saka takunkumin fuska musamman idan za a fita ko Kuma Ana cikin mutane.
6. Za a iya amfani da man tsaftace hannu Idan Babu wura da sabulu domin wanke hannu.
7. A rika zama a dakin dake da iska ko Kuma fanka.
8. A rika tsaftace muhalli akai akai.
9. A rage yawan fita Idan ba ya saka dole ba.
10. A rage yawan Zama wurin da akwai chinkoson mutane.